logo

HAUSA

Yadda kasar Sin take amfana daga yawan al’ummarta ginshiki ne na ci gaban kasar

2021-05-11 21:51:12 cri

Yadda kasar Sin take amfana daga yawan al’ummarta ginshiki ne na ci gaban kasar_fororder_微信图片_20210511213534

A ranar 11 ga watan Mayun nan, hukumar kididdigar kasar Sin ta sanar da sakamakon kidaya al’ummar kasar karo na bakwai, inda aka nuna cewa, a shekarar 2020, yawan jama'ar kasar Sin ya kai biliyan 1.41, wanda ya kai kimanin 18% na jimillar mutanen duniya, kana har yanzu kasar tana kan gaba a duniya a fannin yawan al’umma.

Bayanan sun kuma nuna cewa, kasar Sin na kara saurin sauyawa daga amfani da yawan al’umma zuwa yawan kwararru. Wanda hakan zai ci gaba da karfafa ginshiki na ci gaban kasar.

Ra'ayoyin bainal jama'ar yammacin duniya, suna yin hasashe da tattaunawa sosai kan canjin yanayin yawan al’ummar kasar Sin. Wani muhimmin ra’ayi daga cikinsu shi ne: kasar Sin na fuskantar kalubale biyu na karancin haihuwa da yawan tsofaffi, wanda ka iya hana ci gaban tattalin arzikin kasar. Idan aka yi la'akari da irin bayanan kidaya na baya-bayan nan, ba za a nuna bakin ciki kan hakikanin halin da ake ciki ba.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan mutanen kasar Sin ya karu da miliyan 72.06. Daga cikin su, yawan yaran da shekarunsu ke tsakanin 0-14 ya karu da miliyan 30.92. A halin yanzu kuma, yawan masu iya aiki da shekarunsu ke tsakanin 16 zuwa 59 ya kai miliyan 880, wato har yanzu ma'aikata suna da yawa sosai. Kaza lika matsakaicin shekarun al’ummar kasar ya kai 38.8, kwatankwacin na Amurka.

Kididdigar ta kuma bayyana kyawawan halaye na sauye-sauyen tsarin al’ummar kasar Sin. Ga misali, daga cikin yawan masu aiki, yawan wadanda ke da ilimin sakandare da sama da hakan ya kai miliyan 385, adadin da ya kai kashi 43.79%, wanda ya karu da kaso 12.8 bisa na shekarar 2010.

Girman yawan al’umma, da kuma kyautatuwar ingancin masu aiki, har yanzu suna kasancewa ginshiki na bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin. Wannan shi ma ya ba da tabbaci ga tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Bilkisu)