logo

HAUSA

Bikin Baje Kolin Hajojin Sayayya Na Kasa Da Kasa Karo Na Farko Zai Sa Kaimi Ga Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya

2021-05-11 11:36:56 CRI

Bikin Baje Kolin Hajojin Sayayya Na Kasa Da Kasa Karo Na Farko Zai Sa Kaimi Ga Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya_fororder_0511-1

A jiya ne, aka rufe bikin baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa karo na farko a birnin Haikou na lardin Hainan na kasar Sin, wanda zai inganta kasuwar sayayya ta duniya, da taimaka wajen farfado da tattalin arzikin duniya da samun bunkasuwa. A yayin bikin, kamfanonin kasa da kasa masu halartar bikin sun bayyana cewa, sun koyi fasahohi da kara imani da kansu. Kamfanonin kasar Sin masu halartar bikin su ma sun yi amfani da bikin don gabatarwa duniya kayayyakin Sin masu inganci

Shugaban sashen arewacin Asiya na kamfanin L’Oréal kuma CEO na kamfanin din dake kasar Sin Fabrice Megarbane ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, yadda aka tinkarar cutar COVID-19, ya taimaka wajen raya kasuwar kasar Sin, wadda ta kawo moriya ga dukkan duniya. Gina yankin yin ciniki cikin ‘yanci na Hainan da gudanar da bikin baje kolin hajojin sayayya, wata alama ce dake kara nuna yadda kasar Sin ta kara bude kofarta ga kasashen waje. Ya ce, “Kasuwar Sin ta taimaka ga bunkasuwar tattalin arzikin kamfaninmu, kana sun more fasahohin kasuwanci da sauran kasashen duniya, ta hakan kasuwannin duniya za su amfana daga kasuwar Sin.”

A yayin bikin, kamfanin kiwon lafiya na Omron ya gabatar da sabbin kayayyaki da na’urorinsa na kiwon lafiya. Babbar direktar kula da harkokin yada tambarin kamfanin Wang Ying ta bayyana cewa, “A hakika, kasuwar Sin ta taimaka ga farfado da kasuwannin duniya. Sin ta yi kokari matuka wajen hana yaduwar cutar COVID-19, a shekarar bara, kamfaninmu dake birnin Dalian na kasar Sin ya samar da kayayyakin kiwon lafiya tare da fitar da su zuwa sassan duniya.”

Mataimakiyar shugaban sashen kula da harkokin kasashen waje na kamfanin SHISEIDO dake kasar Sin, Anri Nakahara ta yaba da matakan da kasar Sin ta dauka na hana yaduwar cutar COVID-19, wadanda suka taimaka wajen farfado da tattalin arziki cikin sauri. Ta ce,  “Bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19 a duniya, Sin ta fi daukar matakan da suka dace, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan yaki da cutar, da farfado da tattalin arziki cikin sauri, da kiyaye zaman lafiya da sauransu, kamfanoni masu jarin waje kamar kamfaninmu, muna yaba mata, kana mu yi imani da ci gaba da raya ayyukanmu a kasar Sin. Bayan da aka gabatar da shirin raya yankin ciniki cikin ‘yanci na Hainan, da shirya bikin baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa karo na farko a Hainan, muna da tabbaci kan kyakkyawar makomar kasuwar Hainan, muna fatan samun bunkasuwa tare da Hainan bisa sabbin matakan da aka dauka.”

A yayin bikin, an gabatarwa duniya kayayyaki masu inganci, kana bikin ya samarwa kamfanonin kasar Sin wani dandali mai kyau na shiga kasuwannin duniya.

A yayin bikin, Chen Ping, mai fasahar saka kayayyakin gargajiya ta birnin Yili dake jihar Xinjiang ta kasar Sin, ta kawo kayayyakinta na saka masu alamar kabilarta. A ganinta, bikin baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa, ya taimakawa karin kamfanoni fahimtar al’adun Xinjiang da aka gada daga kaka da kakani, da yadda karin kasashen duniya za su fahimci kayan al’adun kasar Sin.

Mataimakiyar shugaban kwalejin nazari na kungiyar sa kaimi ga yin ciniki ta kasar Sin Zhao Ping ta bayyanawa ‘yan jarida cewa, kamfanonin Sin da na waje sun yi mu’amala da juna a gun bikin baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa, musamman lokacin da masu sayayya suke tuntubar juna, matakin da zai kara fadada kasuwannin duniya, ta hakan za a shaida karin kayayyakin duniya masu inganci da fadada hanyoyin sayar da su. Ta ce, “A yayin bikin baje koli na kasa da kasa kamar bikin baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa, kasashe masu ci gaba da kasashe masu tasowa za su samu damar more fasahohin Sin na bunkasa tattalin arziki, da samar da yanayi mai kyau a wannan fanni. Don haka, bikin zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin duniya bayan ganin bayan cutar COVID-19, baya ga taimakawa kasashen duniya amfani da hanyar da ta dace bayan farfadowar tattalin arzikin duniya.” (Zainab)