Ga yadda sojojin rundunar injiniya na kasar Sin dake tabbatar da kwanciyar hankali a Congo Kinshasa suka gyara titin mota
2021-05-10 09:28:07 CRI
Bisa umarnin da hukumar MDD dake kula da aikin tabbatar da kwanciyar hankali a kasar Congo Kinshasa ta bayar, sojoji fiye da dari na rundunar injiniya ta kasar Sin, ta shawo kan matsalolin da mummunan yanayin cutar COVID-19 suka haifar musu, inda suka yi kwanaki 21 suna gyara wata hanyar mota kamar yadda ya kamata. Ingancin hanyar ya samu yabo daga wajen al’ummar wurin. (Sanusi Chen)