logo

HAUSA

Sin Na Kokarin Taimakawa Afrika Samar Da Isashen Hatsi

2021-05-10 15:01:29 CRI

Sin Na Kokarin Taimakawa Afrika Samar Da Isashen Hatsi_fororder_src=http___y2.ifengimg.com_news_spider_dci_2014_01_a27c89870f31d30a072a9392fd30ac57&refer=http___y2.ifengimg

Gandun gona a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya na cike da aiki yayin da ake kusantar lokacin damina. Manoma a wurin suna tinkarar mawuyacin hali na fama da cutar COVID-19,yayin da kuma suka fara aikinsu na shuka shinkafa karkashin jagorancin masana aikin gona na kasar Sin ta kafar bidiyo.

A cewar Wang Xuemin, wani Basine mai shekaru 53 da haihuwa dake kula da gandun gona mai ba da misali a fannin ayyukan injunan noma a jihar Kebbi, karkashin kamfanin raya aikin gona mai kiyaye muhalli na yammacin Afrika na kasar Sin, wanda ya kwashe shekaru fiye da 10 yana aiki a Najeriya, kasar na da albarkatu ta fuskar ruwan sama da yanayi da haske, kuma ni’imtattun filaye masu fadi na ba ta fifiko matuka wajen gudanar da aikin gona. Wang ya isa Najeriya shekaru 18 da suka gabata, a wancan lokaci, ya damu sosai da rashin ci gaba ta fuskar amfani da injunan aikin gona a wurin. An ce, a lokacin, a kasar Sin, ana amfani da dabaru na zamani wajen ban ruwa don shuka shimkafa, amma a Najeirya, an dogara ne da ruwan sama kadai.

Ba za a iya amfani da dabarun Sin kai tsaye ba a Najeriya, saboda mabambantan yanayi da hanyoyin shuka, sun kasance abubuwan da suka kawo cikas ga aikin samar da shimkafa mai kyau a kasar.

Wang ya ce, guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni, saboda haka, ya yi kokarin bullo da hanyar da ta dace da halin da ake ciki a kasar, bayan ya kwashe shekaru da dama yana neman dabaru masu kyau, yanzu ya warware manyan matsaloli hudu da ake fuskanta a kasar, tare da yin kirkire-kirkire bisa dogaro da hanyar shuke-shuke a wurin, matakan da suka kara yawan shimkafar da ake samarwa.

Wang Xuemin ya yada dabarun fitar da kimiyya da fasahar aikin gona na kasar Sin zuwa kasashen ketare, wadanda su ne: da farko a fahimci yanayin kasa da hanyar shuke-shuke a wurin, daga bisani a gano fifiko da koma bayansu, sa’an nan a yi amfani da kimiyya da fasahar kasar Sin tare da yin kirkire-kirkire.

Abu mafi muhimmanci wajen tabbatar da samar da isashen hatsi a Afrika shi ne, yayata kimiyya da fasahohin Sin a wannan fannin.

Gandun gona da Wang yake aiki, ya ba da damar horar da manoma ta hanyoyi daban-daban, har sauran manoma su kan je wurinsu don koyon fasahohi da sayen iri.

Dubun dubatar manoma na aiki a cikin wannan gandun gona, wasu suna ci gaba da amfani da kimiyya da fasahohin da suka koya daga kamfanin, suna yayata sabbin dabarun shuka shimkafa a duk fadin Najeriya, matakin da ya taimakawa manoman wajen samar da shimkafa mai inganci, a cewar Wang.

Ibrahim Argungu daya daga cikin manoman da suka shiga aikin shuka shimkafa a wannan gandun gona, ya ce, ya gano dalilin da ya sa ba a iya samun shimkafa mai armashi a da, wato akwai bukatar su sauya tunaninsu zuwa amfani da injunan aikin gona.

A shekarar 2015, Ibrahim Argungu ya halarci aijin horar da auren irin shinkafa daban-daban da aka yi a birnin Changsha na lardin Hunan dake kudancin kasar Sin. Ya girgiza saboda ganin kimiyya da fasahohin Sin a cikin wadaccan watanni uku. Ya ganewa idanunsa kimiyya na zamani da Sin take da su musamman a fannin aikin noma. Ya ce, Najeriya na da filaye masu fadi da yanayi mai kyau, amma tana bukatar shigo da hatsi daga ketare a ko wace shekara. Idan aka bullo da kimiyya da fasahohin da suka dace da halin da ake ciki a kasar, kasar za ta iya dogaro da kanta a wannan fanni, har ta fitar da hatsi zuwa sauran kasashe.

Goyon bayan nahiyar Afrika ta fuskar raya aikin noma da samar da isashen hatsi muhimmin aiki ne dake cikin hadin gwiwar Sin da Afrika a ko da yaushe. Yayin taron kolin Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika da aka yi a shekarar 2018, an gabatar da muhimman ayyuka 8, kuma aikin taimakawa Afrika wajen samar da isashen hatsi kafin shekarar 2030 na daya daga cikinsu. (Amina Xu)