logo

HAUSA

Matasa mata biyu na kasar Sin, wato su Liu Liu mai gyara litattafai na zamanin da Han Le, wadda ke aikin shirya fina-finan cartoon

2021-05-09 15:06:33 cri

Kamar yadda aka sani, matasa na iya tabbatar da makomar wata kasa. Yanzu dai a nan kasar Sin, matasa masu yawa na taka rawarsu a fannoni daban daban domin raya kasarsu. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku bayani game da matasa mata biyu na kasar Sin, wato su Liu Liu mai gyara litattafai na zamanin da Han Le, wadda ke aikin shirya fina-finan cartoon.

A cikin babban dakin adana litattafai na birnin Beijing, akwai wasu masu aikin gyara litattafai na zamanin da da yawa, wadanda suke aiki kamar likitocin da ke yin "bincike da ba da jinya" a kan wadannan tsofaffin littattafan masu daraja.

Matasa mata biyu na kasar Sin, wato su Liu Liu mai gyara litattafai na zamanin da Han Le, wadda ke aikin shirya fina-finan cartoon_fororder_刘鎏封面图 无字

Liu Liu mai shekaru 26 da haihuwa, a hankali tana shimfida wani shafi mai launin rawaya na wani tsohon littafi, inda ake iya ganin tsutsotsi masu girman kwayar ridi dake warwatse a kai. Liu Liu da takwarorinta na bukatar hakuri da yin "tiyata" ta musamman a kan wadannan kayayyakin tarihi na dubban shekaru da suka gabata.

"Burushin rubutu, matsefata, abin yin huji a jikin leda, ko katako mai mariki da tsinin baki, wukar gora, dukkansu abubuwa ne da nake bukata a lokacin aiki.  Abubuwan da "likita" mai gyara litattafai na zamani da ya fi bukata su ne, hankali da hakuri da kuma dauriya. ana bukatar makwanni ko watanni da dama domin gyara littafi guda daya.”

Liu Liu ta kara da cewa, akwai wasu abubuwa masu ban sha'awa, kamar akwai talla cikin jaridar daular Qing, da kuma yadda mutane na zamanin da suka gyara rubutunsu, tamkar ina magana da kaka da kakanni ta wannan aiki, na kuma taba gyara wasu zane-zane na zamanin da.

Aikin maido da tsoffin litattafai na kasar Sin na bin hanyar "gyara tsoffin litattafai zuwa kamar tsoffin kaya." Wato manufar aikin ba wai don gyara littafin ba tare da wata matsala ba ne, sai dai don a nuna alamun gyaran ne, kuma a rage tsangwama da asalinsa yadda yake.

Kasancewar akwai bambanci a tsakanin kowane tsohon littafi, da matsayin lalacewarsa, da ingancin takardarsa, yasa hanyoyin gyaransu ma suna da bambanci. Masu gyara littattafai na zamanin da ba wai kawai gyaran littattafai suke yi ba, har ma akwai bukatar su tsara shiri mai dacewa bisa halin musamman na litattafan. Saboda haka, dole ne su samu ilimi a fannin da yawa.

Liu Liu ta yi karatun zane-zane a jami'a, kuma digirinta na biyu ta yi shi ne a fannin ilmin kayayyakin tarihi, da gidan ajiye kayayyakin tarihi.

“Abin da na fi so shi ne zane, na kan je bikin nune-nunen zane-zene, da zane zane bisa yadda mutanen zamanin da suka yi. Daga nan ne, na fara gano cewa, wasu zane-zane da litattafai sun lalace, shi ya sa, nake son gyara su, ta yadda jika da jikokkinmu za su karu daga ilmin mutanen zamanin da.”

Don “ba da jinya yadda ya kamata” ga tsofaffin littattafan "marasa lafiya", Liu Liu tana kokarin koyon ilmi daga tsoffin "likitocin gyara littattafai na zamanin da", kuma a ko da yaushe, tana inganta matsayinta na "ba da jinya", ta yadda za a iya dawo da al'adun gargajiyar masu daraja a kokarin da take yi.

“Yanzu akwai karin matasa dake kula da al'adun zamanin da, bisa kokarin da kasar Sin take yi, wajen karewa da yada al'adun gargajiya. Ina da imanin cewa, za a ci gaba da kiyaye kayayyakin tarihi na kasarmu bisa kokarin da muke yi. ”

Matasa mata biyu na kasar Sin, wato su Liu Liu mai gyara litattafai na zamanin da Han Le, wadda ke aikin shirya fina-finan cartoon_fororder_韩乐

Han Le, ‘yar shekaru 26 a duniya, wadda ke aikin shirya fina-finan cartoon. Kamfanin da take aiki, ya kaddamar da fina-finan cartoon dake samun karbuwa sosai a nan kasar Sin.

A shekarar 2017, Han Le ta shiga kamfanin, saboda sha’awar da take da ita ta kirkirar cartoon a cikin gida. Ayyuka har tsawon shekaru hudu da ta yi a kamfanin, sun sanya ta kara fahimtar wahalar wannan sana'a. Ta ce,

“Gaba daya ana bukatar shekaru 4 wajen hada fim na cartoon. A ganina, masu sana’ar fina-finan cartoon suna da kuzari, musamman ma a lokacin da suke tsara labaran gargajiyar Sin, suna dukufa domin yin aiki mai kyau.”

Matsakaicin shekarun haihuwa na kungiyar aikin ta Han Le, bai wuce shekaru 30 ba. Wadannan matasa ba da dadewa ba, suka dandana faduwar masana'antar cartoon ta kasar Sin. Karfafa wasan kwaikwayo cartoon na kasar Sin ta kokarin da suke yi, ya zama wani mafarki da ke cikin zukatan wadannan matasa.

“Daga aikin rubuta littafin fim zuwa aikin tsara shi da sauransu, akwai mutane da yawa da suka shiga wannan sana’a, daga baya sun fita. Bayan sun gama fim guda daya, amma, fim din bai samu karbuwa sosai ba, sai sun bar aikin. Amma, wasu na ci gaba da aikin. Dalilin shi ne, suna kaunar shi sosai. Fatanmu shi ne, a kara janyo hankalin mutane su kalli fina-finan cartoon na kasar Sin.”