logo

HAUSA

Kada ‘yan siyasar Amurka su ci gaba da yaudarar al’ummun duniya

2021-05-08 17:00:41 CRI

Kada ‘yan siyasar Amurka su ci gaba da yaudarar al’ummun duniya_fororder_xinjiang

Kwanakin baya, kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan Amurka, ya kira taron sauraron ra’ayi kan batun yankin Xinjiang na kasar Sin. An lura cewa, mahalartan taron wadanda suka gabatar da shaidun jabu sun hada da masu neman ‘yancin Xinjiang, da masu adawa da manufofin da kasar Sin take aiwatarwa a yankin, a sakamakon haka, abun da suka yi tamkar wasan kwaikwayo ne na nuna adawa da kasar Sin.

Hakika tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta fara aiki, ta ci gaba da aiwatar da tsohuwar manufar kasar kan kasar Sin, wato tana daukar matakai daban daban domin lalata ci gaban yankin Xinjiang, tare kuma da hana ci gaban kasar Sin. Wani mai amfani da kafar intanet ya yi nuni da cewa, ‘yan siyasar Amurka ba kare hakkin dan Adam na al’ummar Xinjiang suke ba, a maimakon haka lalata shi suke.

Shaidu masu karfi sun riga sun gaskata ci gaban Xinjiang, a cikin shekaru sama da hudu da suka gabata, babu aikin ta’addanci ko sau daya da ya faru a yankin, karkashin kokarin da gwamnatin kasar Sin take yi. Haka kuma, an samu ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma a yankin yadda ya kamata, har matsaikacin karuwar GDP a ko wace shekara tsakanin shekarar 2014 zuwa ta 2019 ta kai kaso 7.2 cikin dari.

Amma wasu ‘yan siyasar kasashen yamma sun yi watsi da hakikanin yanayin da Xinjiang ke ciki, saboda idan suka amince da wadatar yankin, to yunkurinsu na lalata kwanciyar hankalin Xinjiang da hana ci gaban kasar Sin zai bi ruwa.(Jamila)