logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin kayayyakin sayayya na kasa da kasa karo na farko a lardin Hainan

2021-05-07 15:10:20 CRI

A daren jiya 6 ga wata ne aka bude bikin baje kolin kayayyakin sayayya na kasa da kasa karo na farko a birnin Haikou dake lardin Hainan. Sin ta gabatar wa duniya wani dandali mai kyau, na baje kolin kayayyakin sayayya, wanda ya samu halartar kamfanonin Sin da waje kimanin 1500. A gun bikin budewar, masanan kasashen waje sun bayyana fatansu na zurfafa hadin kai da kasar Sin, don more zarafin kasuwannin kasar Sin.

Firaministan kasar Thailand Prayut Chan-o-cha, ya ba da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce manufar tashar ciniki cikin ‘yanci na lardin Hainan da shawarar “ziri daya da hanya daya” sun dace da muradun kasashen biyu, wadanda za su ingiza farfado da kuma bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Ya ce:

“Ina farin ciki sosai da ganin hukumar cinikin kasa da kasa ta kasata, ta sanya hannu kan takardar fahimta tsakanin ta da hukumar kasuwanci ta lardin Hainan, don ingiza hadin kai ta fuskar ciniki, musamman tsakanin kanana da matsakaitann kamfanoni, da kuma a fannin ciniki ta yanar gizo. Ina mai fatan wannan takardar fahimta za ta taimaka wajen karfafa hadin kan kasa ta da lardin Hainan a fannonin ciniki da tattalin arziki.”

An yayyata kasar Switzerland a yayin bikin a wannan karo, don haka Switzerland ta gabatar da kamfanoninta fiye da 20 a Hainan. Shugaban tarayyar Switzerland Guy Parmelin, ya aike da wasikar taya murnar bude bikin, inda ya bayyana fari ciki game da ganin kasar ta zama jigon farko na bikin, yana mai fatan huldar kasashen biyu za ta samu bunkasuwa a dukkanin fannoni.

Jakadan kasar dake Sin Bernardino Regazzoni, ya karanta wasikar a yayin bikin budewar.

“Gayyatar da Sin take baiwa kasar, ta bayyana hulda mai inganci tsakanin kasashen biyu, bisa tushen amincewa da juna. Mun karfafa dangantakar kasashen biyu ta hanyar yin shawarwari da hadin kai, kuma suna kara fahimtar juna a fannoni daban-daban.”

An labarta cewa, jakadu kusan 50 daga kasashen Switzerland da daular hadaddiyar Larabawa, da Indonesiya, da Faransa, da ma sauran kasashe 21 za su halarci bikin.

Babban jami’in reshen yankin Great China, na hukumar ingiza ciniki da zuba jari na gwamnatin Koriya ta Kudu ya ce, hukumar za ta tura kamfanoni 58 don halartar wannan biki, wadanda suka shafi kayayyakin ado, da na’urorin jiyya, da kayayyakin yau da kullum da dai sauransu, yana mai fatan habaka kasuwar kasar Sin ta wannan zarafi mai kyau.

Koriya ta Kudu ce kasar da ta baje tamburanta mafi yawa a yayin bikin a wannan karo. Shugaban hukumar raya tattalin arziki na kasa da kasa na Hainan Han Shengjian ya bayyana cewa,

“Kasashe da yawan tamburan da suke baje a wannan karo ya fi yawa su ne Koriya ta Kudu, da Faransa, da Japan, da Amurka, da Italiya, inda adadin na su ya kai 124, da 99, da 89, da 68 da kuma 56.”

An ba da labarin cewa, yawan fadin bikin ya kai murabba’in mita dubu 80, wanda ya zama bikin baje kolin kayayyakin sayayya mafi girma da inganci a yankin Asiya-Pacific. A cikin sa, wurin baje kolin kayayyakin sayayya na ketare ya kai murabba’in mita dubu 60, inda ake baje kolin kayayyakin yau da kullum, lu’u lu’u da kayayyakin gina jiki, da kayayyakin bude ido, da na ba da hidima. Shugaban sashin kula da harkokin sayayya na hukumar kasuwancin kasar Sin Zhu Xiaoliang ya ce:

“Bikin baje kolin na nacewa ga ka’idar samun ci gaba da bude kofa, a kokarin da yake yi na koyon yadda sauran bukukuwan baje kolin kasa da kasa suke tafiya, wajen zama wani bikin baje koli mai muhimmanci a duniya, dake iya baiwa kayayyakin duniya wani zarafi mai kyau na shiga kasuwannin kasar Sin, da sayar wa kayayyakin kasar Sin da na kasa da kasa zuwa sassa daban daban na dniya.”

An ba da labarin cewa, a yayin bikin, kamfanonin kasa da kasa za su shirya harkoki 81 don gabatar da kayayyaki fiye da 100, ciki hadda tufafi, da kayayyakin ado, da abinci, da abin sha da lu’u lu’u da sauransu. (Amina Xu)