logo

HAUSA

Yan siyasar Australia masu adawa da Sin za su debo ruwan dafa kansu

2021-05-07 21:51:44 CRI

Yan siyasar Australia masu adawa da Sin za su debo ruwan dafa kansu_fororder_澳大利亚

Wani sharhi da wani Ba-Amurka mai suna Bradley Blankenship ya wallafa a shafin Intanet na “Russia Today” ya nuna cewa, kasar Australia za ta girbi abin da ta shuka, kan gurguwar shawarar da ta dauka game da alakarta da kasar Sin.

Sharhin ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta sanar da dakatar da duk wasu ayyuka karkashin tattaunawar tattalin arzikin bisa manya tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, har sai illa masha Allahu. ‘Yan bokon kasar Australia dai, suna son harzuka kasar Sin, matakin da ba zai haifarwa kasar kyakkyawan sakamako ba.

Kamar yadda Blankenship ya bayyana a cikin sharhin, wasu ‘yan siyasar Australia, da jagororin soja, da masu dauko rahotanni, a baya-bayan sun rika yin kalaman tayar da jijiyar wuya kan alakar Sin da Australia. Musamman, bangaren na Australia, ya yi amfani da, wai “batun tsaron kasa” domin takaita da ma dakatar da ayyuka da nasarorin da aka cimma a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da fannin da ya shafi bil-adama, da sauran fannoni tsakanin Sin da Australia, matakin da ya lalata amincewa da juna tsakanin kasashen biyu, da lalata tushen musaya da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Wajibi ne wadannan ‘yan siyasar kasar ta Australia wadanda ke da tunanin yakin cacar baka, su fahimci cewa, kasar Sin ba za ta taba bari su yi amfani da kasar Sin su gudanar da ayyukan siyasa don nuna jinin kasar Sin ba.(Ibrahim)