logo

HAUSA

Yan siyasar Amurka suna yaudarar al’ummun kasa da kasa

2021-05-07 19:51:04 CRI

Yan siyasar Amurka suna yaudarar al’ummun kasa da kasa_fororder_2

A kwanakin baya ne aka kammala taron ministocin harkokin wajen kasashe mafiya karfin tattalin arziki wato G7 a Landan na Birtaniya, kamar yadda ake zaton, kasar Sin ta sake jawo hankalin duniya matuka. Yayin taron, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa, kasarsa ba hana ci gaban kasar Sin ta ke yi ba, a maimakon haka, tana kare tsarin kasa da kasa, kamar yadda ka’idojin kasa da kasa suka tanada, amma tsokacinsa babu dalili ko kadan, saboda Amurka tana lalata tsarin kasa da kasa, bai kamata ba ta bukaci sauran kasashe su martaba tsarin ba.

Tun daga watan Janairun bana wato bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta fara aiki, ta rike yin tsokaci kan ka’idoji ko tsarin kasa da kasa, amma yanzu kwanaki dari daya kawai da suka shude, an lura cewa, ka’idojin Amurka ka’idojin nuna fin karfi ne, kuma manufar cudanya tsakanin sassa daban daban ta Amurka, wani rukunin siyasa ne da ta kafa.

Misali ka’idar rashin tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, ka’ida ce mafi muhimmanci da aka tsara a cikin ka’idojin MDD, amma har yanzu, Amurka ba ta daina tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe ba.

Kana Amurka tana mayar da kungiyoyin kasa da kasa a matsayin wurin wasa, inda take shiga ko fita kamar yadda take so, kana tana kalubantar hukumar kiwon lafiya ta duniya da kungiyar cinikayya ta duniya da sauransu.

Hakika tsarin kasa da kasa daya ne kacal a duniya wato shi ne tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin MDD, kuma akwai tsarin ka’idojin kasa da kasa daya kawai a duniya wato tsarin ka’idojin daidaita huldar kasa da kasa da aka tsara bisa tushen ka’idojin MDD, wajibi ne wasu kasashen yamma wadanda ke matsa wa sauran kasashe lamba bisa fakewa da ka’idoji su martaba ka’idojin kasa da kasa yadda ya kamata.(Jamila)