logo

HAUSA

A watan Maris rarar kudaden cinikayyar Sin sun kai yuan biliyan 60.9

2021-05-06 12:33:42 CRI

Wasu alkaluman kididdiga da hukumar lura da harkokin musayar kasashen waje ta kasar Sin ta fitar, sun nuna cewa, a watan Maris din da ta shude, adadin rarar kudaden cinikayyar hajoji da hidimomi na kasa da kasa da Sin ta samu, sun kai kudin kasar yuan biliyan 60.9, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9.42.

Kaza lika kudaden cinikayyar da kasar ta samu sun kai sama da yuan tiriliyan 1.72, yayin da kudaden da aka kashe a fannin suka kai yuan tiriliyan 1.66.

Hukumar ta kara da cewa, kudaden shiga daga cinikayyar hajojin kasar Sin sun kai yuan tiriliyan 1.54, haka kuma an kashe yuan tiriliyan 1.43 a fannin, wanda hakan ya samar da rarar yuan biliyan 116.8.

A daya bangaren kuma, fannin cinikayyar ba da hidima ta samu raguwar yuan biliyan 55.9, yayin da kudaden shigar da Sin ta samu a fannin suka kai yuan biliyan 177.8, kana kudaden da aka kashe a fannin sun kai yuan biliyan 233.8 .(Saminu)