logo

HAUSA

Nahiyar Afirka Ba Za Ta Taba Yin Watsi Da Moriyar Da Take Samu Daga Alakar Ta Da Sin Ba

2021-05-06 19:13:14 CRI

Nahiyar Afirka Ba Za Ta Taba Yin Watsi Da Moriyar Da Take Samu Daga Alakar Ta Da Sin Ba_fororder_210506-Sharhi-Saminu-hoto

Cikin ’yan kwanakin nan, daya daga muhimman batutuwa dake jan hankalin masharhanta shi ne, kalaman da sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya furta, yayin da yake zantawa ta kafar bidiyo da wasu shugabanni, da ministocin harkokin wajen Najeriya da Kenya, da kuma wasu daliban Afirka, wadanda suka taba karatu a Amurka.

Cikin kalamansa, Mr. Blinken ya ja hankalin kasashen Afirka da su yi taka tsantsan da yadda suke cudanya da kasar Sin, yana mai yayata ra’ayoyin Amurka, na zargin kasar Sin da kasancewa wai barazana ga sauran sassa. Kana wai kasashen Afirka su yi a hankali, kar su fada tarkon bashin kasar Sin. A hannu guda ya zargi Sin din ya tattare damammaki da ya kamata a ce al’ummun nahiyar Afirka sun samu.

To amma fa, masu fashin baki da dama na kallon wadannan kalamai na Mr. Blinken, a matsayin dabaru da Amurka ke kokarin aiwatarwa, na gurgunta alakar Sin da kasashen nahiyar Afirka, ta yadda Amurkar za ta ci gaba da bunkasa tasirinta ita kadai a nahiyar.

Masana da dama na ganin wannan manufa ta Amurka ba za ta yi nasara ba, duba da yadda kasashen Afirkan ke ganin moriyar alakarsu da Sin a zahiri. Alal misali, a baya bayan nan, tun bayan barkewar cutar numfashi a sassan duniya baki daya, tallafi mafi yawa, kuma cikin gaggawa da kasashen Afirka suka samu domin shawo kan cutar COVID-19, ya fito ne daga kasar Sin. Kaza lika Sin ta goyi bayan shirin COVAX na samar da rigakafi ga kasashe masu rauni, wanda ke gudana karkashin hukumar lafiya ta duniya WHO. Baya ga kyautar rigakafin cutar da Sin ta samarwa kasashen nahiyar da dama.

Amma kafin zuwan wannan annoba ma, idan mun waiwayi baya, za mu ga irin yadda dangantakar Afirka da Sin ke yaukaka, karkashin dandalin FOCAC na hadin gwiwar sassan biyu. Gwamnatin Sin ta fitar da manufofi iri daban daban, na samarwa kasashen nahiyar rance gata, da karfafa gwiwar kamfanonin Sin su zuba jari a nahiyar, ta yadda harkokin zuba jari na kai tsaye, da na cinikayyar kasa da kasa tsakanin sassan biyu za ta ci gaba da fadada. Cikin sauki, kowa na iya fahimtar manufar Sin a wannan fanni, duba da cewa, Sin din ba ta dauki alakarta da Afirka a matsayin wata harkar takara ba. Wato ba wasu shaidu dake nuna Sin tana adawa, ko takara da kasashe irin su Amurka, da Faransa, da Birtaniya, wadanda suka jima suna cudanya da nahiyar Afirka.

Sin ta taka rawar gani wajen samar da manyan ababen more rayuwa, kamar manyan titunan mota, da layukan dogo, da filayen jiragen sama, da tashoshin jiragen ruwa, da makarantu, da asibitoci. Ta kuma sha tura jami’an kiwon lafiya domin gudanar da ayyukan jin kai zuwa sassan Afirka. Kari kan haka, ta taimaka wajen samar da yankunan masana’antu da sauran su. Don haka ko shakka babu, al’ummar nahiyar Afirka ba za ta taba yin watsi da moriyar da suke samu daga alakarsu da Sin ba. Kuma lokaci ya yi, da Amurka za ta dawo daga rakiyar manufofinta na shafawa kasar Sin kashin kaji, tun kafin ta sha karin kunya a idanun duniya! (Saminu Hassan)