logo

HAUSA

Sayayya a hutun ranar ma’aikata ta shaida habakar kasuwar kasar Sin

2021-05-06 19:26:23 CRI

Sayayya a hutun ranar ma’aikata ta shaida habakar kasuwar kasar Sin_fororder_sayayya-1

A lokacin hutun ranar ma’aikata ta kasa da kasa na tsawon kwanaki biyar wato tsakanin ranar 1 zuwa 5 ga wata, sayayya da aka yi a kasuwar kasar Sin ta bai wa duk duniya mamaki matuka, alkulama sun nuna cewa, gaba daya adadin mutanen da suka fita waje domin yawon shakatawa a fadin kasar ta Sin ya kai miliyan 230, adadin da ya karu da kaso 119.7 cikin dari a kan makamancin lokacin bara, kuma adadin kudin shigar da aka samu daga sana’ar yawon shakatawa, ya kai kudin Sin yuan biliyan 113.23, adadin da ya karu da kaso 138.1 cikin dari idan aka kwantanta da makamancin lokacin bara.

Hakika sayayya a lokacin hutun ranar ma’aikata ta shaida cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen kandagarkin annobar COVID-19, haka kuma ta nuna cewa, kasuwar sayayya ta kasar Sin tana farfadowa, biyo bayan managartan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, wajen ingiza sayayya, da kara kudin shigar al’ummun kasar, da kuma kyautata yanayin sayayya, a sakamakon haka, boyayyen karfin sayayya na kasar Sin yana kara habaka, har yana samarwa duniya damammaki.

Hakazalika, za a shirya bikin baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa na kasar Sin karo na farko a lardin Hainan, tsakanin ranakun 7 zuwa 10 ga wata, inda aka kebe wurin baje koli mai fadin muraba’in mita dubu 60 ga ‘yan kasuwan ketare, wanda zai kai kaso 75 cikin dari na daukacin wuraren baje lolin, daga bikin baje kolin Canton Fair, zuwa bikin CIIE, da bikin hada-hadar ba da hidimomi, da kuma bikin hajojin sayayya, matakin dake nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana cika alkawarinta na mayar da kasuwar kasar Sin a matsayin kasuwar duniya, ta hanyar daukar hakikanin matakai.(Jamila)