logo

HAUSA

Matasa Kashin Bayan Ci Gaban Al’umma

2021-05-05 19:09:30 CRI

Matasa Kashin Bayan Ci Gaban Al’umma_fororder_210505-sharhi-Ibrahim-hoto

Matasa dai su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma, wannan nema ya sa mahukuntan kasar Sin suka kebe ranar 4 ga watan Mayun kowace shekara a matsayin “Ranar Matasa ta Kasa”. Saboda muhimmancin matasa ga ci gaban kowace kasa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha nanata cewa, idan har yara manyan gobe suna da manufofi da kwarewa da nauyi, hakika kasa tana da makoma da kuma fata.

Ita dai wannan rana, ta samo asali ne, a ranar 4 ga watan Mayun shekarar 1919, lokacin da wasu matasa masu kishin kasar Sin suka shirya gangamin yaki da mulkin danniya da aka yi wa kasar.

A matsayinsa na tsohon dalibin sahararriyar jami’ar nan ta Tsinghua ta kasar, Xi jinping ya taba ziyartar jami’a, har ma makarantun midil albarkacin wannan rana ta matasa, don tunasar da su muhimmancin mayar da hankali ga harkokinsu na karatu da yadda za su cimma burin da suka sanya a gaba, har ma su bayar da gudummawa ga ci gaban kasa.

A lokacin ziyarce-ziyarce nasa, Xi Jinping ya tsara wani kundin raya ilimi mai zurfi na kasar Sin da kara fatan da yake da shi kan dalibai matasa, inda ya bukace matasa, da su rungumi burin da ake da shi a tarihi, su kara kaimi na zama jaruman sabon karni a matsayin muhimmin aiki na cimma burin farfado da kasa.

Xi ya kara da cewa, inganci da kokarin matasa yana shafar matakan cimma mafarkin kasar Sin. Ya kuma sha yiwa dalibai matasa bayani a lokuta da dama game da hanyar koyo, inda ya jaddada cewa, “Wajibi ne a koyi ilimi kamar yadda soso yake tsotse ruwa” domin karfafa ma’anar gaggawa a tsarin koyo.

Albarkacin wannan rana mai muhimmanci, shugaba na kasar Sin ya bayyana cewa, matasa za su tabbatar da makomar huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, saboda haka kasar Sin na kokarin taimakawa matasan bangarorin 2, don samar musu da karin guraben aikin yi, da damammaki na raya kansu.

A don haka, shugaba Xi yana fatan dalibai ’yan Afirka dake karatu a kasar Sin, za su yi kokarin koyon ilimi, ta yadda za su daukaka hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi.

Baya ga kasancewarsu jigon ci gaban kasa, matasa na iya zama wata gada dake sada zumunta, da musanyar kwarewa da fasashohi, da al’adu da kasuwanci da sauransu tsakanin kasashe da al’ummominsu. Wai albarkacin kaza, kadangare kan sha ruwan kasko. (Ibrahim Yaya)