logo

HAUSA

Amurka: Mai hali ba ya canjawa

2021-05-04 21:35:41 CRI

Amurka: Mai hali ba ya canjawa_fororder_amurka

A jiya ne, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa birnin London na Burtaniya, don halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen nan bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7. Kamar yadda aka yi zato, ziyayar Blinken ba wani boyayyen abu ba ne, game da anniyar Amurka ta mayar da kasar Sin da Rasha saniyar ware. Wannan na faruwa ne, yayin da gwamnatin Biden ke cika kwanaki 100 a kan mulki, ta kuma kara bayyana yadda ta yiwa manufofinta na diflomasiya gyare-gyare.

Tun bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta kama aiki, duniya ta kara nuna damuwa, kan yadda ta ke tafiyar da kasar dake fama da rarrabuwar kawuna. Yanzu dai amsar hakan ya fito fili: Tuni Amurka ta sauya alkibarta game da batun shiga tsakani, kafin ta kammala janye sojojin baki daya daga kasar Afghanistan.

Har yanzu Amurka tana fakewa da batun kare hakkin dan-Adam, demokidariya, da ‘yanci, tana ci gaba da hada kai da kawayenta don matsawa kasar Sin lamba. Amma tarihi tamkar madubi ne. Bayan gwamman shekaru na gwagwarmaya a yankin Gabas ta Tsakiya, Amurka ta kare cikin rashin nasara. A Asiya, abu ne mai matukar hadari, a tsoma baki cikin kasa mai karfi kamar kasar Sin.(Ibrahim)