logo

HAUSA

Tashar NHK ta Japan: A Sin an gudanar da bikin ranar kwadago tamkar na shekarar 2019

2021-05-03 15:57:11 CRI

Tashar NHK ta Japan: A Sin an gudanar da bikin ranar kwadago tamkar na shekarar 2019_fororder_NHK

Tashar gidan talabijin ta NHK dake kasar Japan, ta ce yanayin gudanar da bikin ranar kwadago, da shagulgulan hutun bikin na bana a kasar Sin, ya yi kama da wanda kasar ta gudanar a shekarar 2019 gabanin bullar cutar COVID-19. Inda daruruwan miliyoyin Sinawa suka yi tafiye tafiye, yayin hutun wannan biki na kwanaki 5.

Kafar ta NHK ta ce, gwamnatin Sin ta yi hasashen sake farfadowar al’amura a bangaren zirga zirgar matafiya a sassan kasar. Musamman duba da yadda Sinawa da dama suka gaza samun damar saduwa da iyalan su, ko komawa garuruwan su, yayin bikin bazara da ya gabata a watan Fabarairu, bisa amincewa da shawarar takaita tafiye tafiye da gwamnati ta gabatar.

Ma’aikatar sufurin kasar Sin ta yi hasashen cewa, za a gudanar da tafiye tafiye da yawan su ya kai miliyan 265, yayin wannan biki na ranar ma’aikata, wanda hakan ya yi kusa da adadin da kasar ta samu kafin bullar annobar COVID-19 a shekarar 2019.

Yanzu haka dai kwanaki 10 ke nan, ba a samu sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19 a kasar Sin ba, in banda wadanda ke shigowa da cutar daga kasashen ketare.  (Saminu)