logo

HAUSA

Masanin IMF: An Yabawa Yadda Sin Ke Tinkarar Cutar COVID-19

2021-05-03 16:53:26 CRI

Masanin IMF: An Yabawa Yadda Sin Ke Tinkarar Cutar COVID-19_fororder_210503-sharhi-Ahmad-hoto

Masu hikimar Magana na cewa “yabon gwani ya zama dole”. Tun bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 gwamnatin kasar Sin ta himmatu gami da sa kaimi wajen tinkarar annobar wacce ta zamewa duniya babbar damuwa, musammna irin jerin matakan da kasar ta dauka na yin kandagarki domin dakile tasirin annobar. Sai dai za mu iya cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu, musamman duba da irin manyan nasarorin da kasar ta cimma a yaki da annobar. Ko shakka babu, wadannan nasarorin sun ja hankalin al’ummomin duniya, musamman hukumomi da kungiyoyin kasa da kasa. Ko da a kwanakin baya sai da wani jami’in asusun bada lamuni na kasa da kasa wato IMF ya bayyana cewa kasar Sin ta cancanci yabo game da yadda take tinkarar annobar COVID-19, kana ta kuma taka rawar gani game da magance manyan kalubaloli. Kafar yada labaran CNBC ta rawaito Tobias Adrian, daraktan sashen kasuwannin hada hadar kudade na hukumar IMF yana cewa, kasar Sin ta yi nasarar dakile annobar ta hanyar amfani da kwararan matakai, kuma a kan lokacin da ya dace ba tare da jan kafa ba. Adrian ya fadawa kafar yada labaran CNBC cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya riga ya koma yanayi mai kyau tun a tsakiyar shekarar da ta gabata, kuma yana sama da na ragowar dukkan kasashen duniya. Ko da yake, har yanzu mahukunta kasar Sin ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin dakile annobar duba da yadda aikin riga-kafin cutar ke cigaba da kankama a duk fadin kasar, kamar yadda a makon da ya gabata mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan, ta yi kira da a hanzarta samarwa da raba alluran riga kafin COVID-19, tare da tabbatar da inganci da tsaro da kara yi wa jama’a riga kafin, don gina garkuwa na hana kamuwa da cutar. Sun, wadda har ila yau mambar hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta bayyana haka ne, lokaci da ta duba yadda ake yiwa jama’a riga kafin, da ma samar da shi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Yayin ziyarar uwar gida Sun, ta kuma ziyarci wurin da ake yiwa jama’a riga kafi a birnin, inda ta kalli tsari da hidima da matakan tsaron da aka samar game da yiwa jama’a riga kafin. Ta kuma lura da cewa, gangamin riga kafin shi ne mafi girma, tun bayan kafa sabuwar kasar Sin, inda aka kafa cibiyoyin yin riga kafi sama da 50,000 a sassan kasar, kuma ya zuwa yanzu, an yiwa sama da mutane miliyan 240 alluran. A don haka, Sun ta yi kira da a kara kaimi, don tabbatar da tsaron riga kafin ga jama’a, a kuma ilmantar tare da fadakar da jama’a game da riga kafin. Da ma ‘yan Magana kan ce “da zafi-zafi a kan bugi karfe.”(Ahmad Fagam)