logo

HAUSA

Ba kasar da ke rike da tambarin tada husuma sama da Amurka

2021-05-03 21:28:18 CRI

Ba kasar da ke rike da tambarin tada husuma sama da Amurka_fororder_1

Yayin zantawa da wata kafar watsa labarai ta Amurka a jiya Lahadi, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya zargi kasar Sin da cewa wai, tana kara wuce gona da iri a waje, da nufin kasancewa mafi karfin fada a ji a duniya. Kalaman da ke jaddada zargin da Amurka ke yiwa kasar Sin na zama barazana, duk dai da nufin biyan bukatun siyasar kashin kai.

Ga alama dai a idanun wasu Amurkawa, wasu kasashe na daban na wuce gona da iri, idan har suna aiwatar da manufofin ci gaban su na halal, yayin da ita kuma Amurka ke ci gaba da aiwatar da na ta manufofin na siyasar matsin lamba a duk inda ta so. Wannan salo na daukar matsaya biyu, wanda aka dade da sanin Amurka da shi, na kara nuna burin ta na yin mulkin danniya.

To sai dai kuma, Amurka ba ta da damar tsara yadda ya kamata duniya ta kasance. Sanin kowa ne cewa, a boye Amurka na yunkurin maye gurbin dokokin kasa da kasa da na ta salo, karkashin matakan ta na ba da tallafi.

Cikin gwamman shekaru, Amurka ta aiwatar da matakai na zahiri, domin bayyana halayyarta, ta cimma buri ta hanyar diflomasiyyar tursasawa, ciki har da amfani da karfin barazana, da mayar da wasu saniyar ware a siyasance, da kakaba takunkumin tattalin arziki, da dakile ci gaban sashen fasahar wasu.

Alal hakika, kasashe masu ‘yanci manya da kanana, masu karfi da raunana, na da matsayi na bai daya karkashin dokokin kasa da kasa, ba kuma wanda ke da aniyar kabar kaskanci.

Ba da jimawa ba, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta fayyace yayin wani taro ta kafar bidiyo na manema labarai, bayan taron shugabannin kungiyar tarayyar Turai ta EU, cewa Turai na da bukatar manufofin kasar Sin na kashin kan ta. Kuma Amurka ba za ta yi nasara a matsin lambar da take yiwa sassan kasa da kasa ba.  (Saminu)