logo

HAUSA

Jami’in MDD yayi maraba da matakin maido yarjejeniyar zaben Somali

2021-05-02 15:45:38 CRI

Jami’in MDD yayi maraba da matakin maido yarjejeniyar zaben Somali_fororder_0502-somali

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da kudirin da majalisar wakilan kasar Somaliya ta dauka, na soke dokar zaben tarayyar kasar, kana ta dawo da tsarin yarjejeniyar zaben kasar wadda aka cimma matsaya a ranar 17 ga watan Satumbar 2020, kakkain babban sakataren ya bayyana hakan.

A sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, babban sakataren ya jaddada yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a kasar Somali da su koma kan teburin tattaunawa ba tare da bata lokaci ba, kana su yi kokarin cimma daidaito wajen gudanar da zaben da ya shafi dukkan bangarorin kasar ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma nanata muhimmancin kulla yarjejeniyar da dukkan bangarori da nufin samun zaman lafiya a kasar.

A ranar Asabar majalisar wakilan kasar ta kada kuri’ar soke tsawaita wa’adin mulkin shugaban kasar, wanda aka ayyana a ranar 12 ga watan Afrilu, wanda ya bada damar tsawaita wa’adin majalisar zartarwar kasar da na wakilan majalisar tarayyar kasar zuwa shekaru biyu masu zuwa.

Shugaban kasar Mohamed Farmajo, wanda ya gabatarwa majalisar wakilan kasar jawabi gabanin jefa kuri’ar, ya bukaci ‘yan majalisar da su maido da yarjejeniyar da aka cimma ta ranar 17 ga watan Satumbar 2020, yarjejeniyar wacce aka amince da ita tsakanin gwamnatin tarayya da shugabanni biyar na hukumar tarayyar jahohin kasar.(Ahmad)

Ahmad