logo

HAUSA

Tashar sararin samaniyar Sin za ta kasance ta dukkanin Bil Adam

2021-04-30 13:56:16 CRI

Tashar sararin samaniyar Sin za ta kasance ta dukkanin Bil Adam_fororder_微信图片_20210430135516

Jiya Alhamis, Sin ta harba rukunin tauraron dan adam na Tianhe ta hanyar amfani da rokar dakon kaya na CZ-5B Y2, wanda kuma yana kama hanyarsa ta zuwa sararin samaniya kamar yadda aka tsara. Abin da ya alamta cewa, Sin ta fara aikinta na gina tashar binciken sararin samaniya na kashin kanta.

Sin ta taka muhimmiyar rawa a wannan karo a fannin gina tashar dindindin, matakin da duniya baki daya za ta ci gajiya. Ana tunanin cewa, tashar binciken sararin samniya ta kasa da kasa wadda ta dade tana aiki a sararin samaniyar har shekaru fiye da 10, watakila za ta daina aiki tsakanin shekarar 2024 zuwa 2028, a lokacin tashar Sin ce daya tilo, da bil-Adama zai yi amfani da ita wajen bincike a sararin samaniya.

Sabanin wasu tsirarrun kasashen yamma, kasar Sin tana nacewa da yin amfani cikin lumana, da daidaito, samun nasara da ci gaba tare, da kuma gina tashar binciken sararin samaniya na Sin a matsayin wani dandali ga al’ummar duniya dake iya hadin kan kasa da kasa da yin mu’amala da musaya cikin ‘yanci a fannin kimiyya da fasaha tsakanin kasashen duniya.

Hadin kai da Sin take yi dangane da wannan tashar, yana mai da hankali matuka ga bukatun kasashe masu tasowa dake da karancin kudade da kimiyya, don ba su wata damar shiga sararin samaniya, ta yadda za su gudanar da aikin gwaje-gwaje a wannan fanni, a don haka tashar za ta zama gida ga kasashe masu tasowa. Matakain da zai taimaka wajen cike gibin dake tsakanin kasashen duniya ta fuskar bunkasuwar kimiyya da fasaha, ta yadda kasashen duniya za su samu dama baki daya wajen shiga aikin bincike da amfani da sararin samaniya. (Amina Xu)