logo

HAUSA

Japan ta kama hanya mai kuskure kan huldarta da kasar Sin

2021-04-29 11:08:11 CRI

Japan ta kama hanya mai kuskure kan huldarta da kasar Sin_fororder_微信图片_20210429110614

 

A kwanakin baya ne, ma’aikatar harkokin wajen kasar Japan ta fitar da wani bayani kan ayyukan diplomasiyya na shekarar 2021, wanda ya rura wutar takaddama kan tsibirin Diaoyu da tsoma baki kan batun tekun Nanhai da yankin Hongkong da na Xinjiang da dai sauransu, da kuma yada karya wai “Sin tana zama barazana”, a hannu guda kuma, bayanin ya mai da huldar kasashen biyu a fannin tattalin arziki a matsayin dangantaka mafi muhimmanci tsakanin bangarori biyu. Sabani dake tsakanin manufar siyasa da tattalin arziki ya sa manufofin da gwamnatin Japan ke dauka kan kasar Sin ba sa dorewa, abin da ya tilasta gwamnatin sauya manufofin da ta dauka kan kasar Sin.

Firaministan Japan Suga Yoshihide, wani tsohon dan siyasa ne. An kuma yaba masa cewa, yana da kwarewa matuka wajen tafiyar da harkokin siyasa. Amma, matakan da ya dauka kan kasar Sin a ’yan watannin baya sun bayyana cewa, rashin fahimtarsa game da huldar kasashen biyu, alal misali, tattaunawar bangarori hudu na Amurka da Japan da India da Austriliya a watan Maris, da tattaunawar Amurka da Japan na 2+2 da haddadiyar sanawar da shugabannin Amurka da Japan suka fitar a watan Afrilu da ma wannan bayani game da huldar kasa da kasa.

Sauyin tunanin da gwamnatin Japan ta yi, yana da alaka da kawancen dake tsakaninta da Amurka da kuma halin da ake ciki yanzu. Tun hawansa kujerar firaministan kasar a watan Satumban bara, Suga Yoshihide bai samu karbuwa sosai ba a kasar. Sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar, saboda rashin daukar matakan da suka dace wajen yakar cutar COVID-19, kafofin yada labarai na kasarsa sun fara tattauna kan batun zabar sabon dan takarar firaminista na gaba tun daga watan Jarairu na bana.

Bayan da Joseph Biden ya zama shugaban Amurka, ya mai da kasar Sin a matsayin babbar ’yar takararta a duniya, inda ya dauki manufar dakile kasar Sin ta hanyar kulla kawance, matakin da ya baiwa Suga Yoshihide da ministansa wannan dama. A ganinsu, zama inuwa guda da Amurka ba ma kawai zai kara karfinsu na matsa lamba ga kasar Sin ba, har ma zai ba shi damar neman zarcewa kan mukaminsa.

Amma, a hakika dai tattalin arzikin Japan na matukar dogaro da kasuwannin kasar Sin, ko da yake Japan da Amurka sun kulla kawance kut da kut amma matakin da zai samar mata moriyar tattalin arziki ba mai kyau ba ne. Wannan shi ne dalilin da ya sa ake daukar huldar Sin da Japan a matsayin wata muhimmiyar hulda ta bangarori biyu mafi muhimmanci a duniya a cikin bayanin da Japan ta gabatar.

Yawan kayayyakin da Japan ta fitar a shekarar 2020 ya ragu da kashi 11% saboda yadda cutar COVID-19 take kan ganiyarta, duk da haka yawan motoci da na’urar da suka shafi laturoni ba gaba daya da Japan ta fitar zuwa Sin ya karu da kashi 3%. A cikin shekaru 20 da suka gabata, yawan kayayyakin da Japan ya fitar zuwa Sin ya kai kimanin 10% na dukkanin kayayyakin da ta fitar, amma yanzu wannan adadi ya kai 22% a shekarar 2020, kaso 17% kawai kan na Amurka. Yawan ribar da Japan ta samu daga kasar Sin a wannan fanni ya kai 17%, yayin da na Amurka kuma bai wuce 5% ba.

Sin da Japan na cikin mabambanta matakan bunkasuwa, amma suna da kyakkyawar damar hadin kai da cin moriya tare. Japan ba za ta debi mata daga koma baya na shekaru 20 ba, inda ta gaza samun hadin kai da kasar Sin a fannin tattalin arziki.

Duk da adawar da Japan ke yiwa Sin a fannin siyasa, da sabanin da suke da shi a wasu fannoni, amma tana matukar dogaro da kasar Sin a fannin tattalin arziki. Amma, jita-jita da take bazuwa wai Sin tana zama barzana, zai kawo illa ga ciniki da zuba jarinta a Sin. Sin ba za ta yarda da yadda Japan take nuna fuska biyu kan huldar kasashen biyu ba, kuma yunkurin gwamnatin Suga Yoshihide ba zai cimma nasara ba.

Ya kamata, Japan ta fahimci cewa, matakan da take dauka bisa damar da take da ita tsakanin Sin da Amurka ba za su kawo wa kasarta moriya ba ko kadan. Dole ne Japan ta koma hanyar da ta dace, ta sake nazarin huldarta da kasar Sin. (Amina Xu)