logo

HAUSA

Harba bangaren tashar sararin samaniya na Tianhe muhimmin ci gaba ne ga burin kasar Sin na zurfafa ayyukan sama jannati

2021-04-29 15:38:09 CRI

Harba bangaren tashar sararin samaniya na Tianhe muhimmin ci gaba ne ga burin kasar Sin na zurfafa ayyukan sama jannati_fororder_0429-1

Yayin da manyan kasashen duniya ke ci gaba da zurfafa kwazonsu, a fannin binciken sararin samaniya, kuma manyan kasashe ke cimma karin nasarori a wannan fanni, kasar Sin na ci gaba da bin sahu, a yunkurin ta na kafa tashar binciken sararin samaniya ta kashin kanta, nan da karshen shekarar 2022 dake tafe.

Kafin wannan lokaci, Amurka da Rasha ne kasashe biyu kadai, da suka taba kafa tashoshin binciken sararin samaniya na kashin kansu. Daga bisani a shekarar 2003, Sin ta cimma nasarar harba kunbon sama jannati mai dauke da bil adama. Wanda hakan ya sanya ta kafa wani muhimmin tarihi a wannan fanni.

Kaza lika, kafin harba bangaren tashar samaniya na Tianhe, Sin ta taba harba wasu tashoshin gwaji guda biyu, wato Tiangong-1 da Tiangong-2, wadanda suka baiwa ’yan sama jannati na kasar damar kasancewa a tashar na dan lokaci.

Bahaushe kan ce “Jumma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”. Masharhanta da dama na kallon harba sashen tashar samaniya na Tianhe, a matsayin muhimmin aiki da ke alamta nasarar da Sin za ta samu, a fannin binciken sassan sararin samaniya, bayan kammala tashar da take ginawa.

Bisa tsarin aikin wannan bangare na tashar samaniya, za a yi amfani da Tianhe tsawon shekaru 10 ne, ko da yake ana hasashen zai iya zarta hakan, idan an kula, tare da aiwatar masa da gyare gyare. Ana kuma hasashen kammala kafuwar wannan sabuwar tashar samaniya mallakar kasar Sin, bayan harba karin sassan ta kimanin guda 10 a nan gaba.

Sabuwar tashar samaniya mallakar kasar Sin, za ta kafa muhimmin tarihi, a fannin bunkasa binciken duniyoyin dake wajen duniyar bil adama, duba da cewa, tasha daya tilo da ake da ita a yanzu haka, wato tashar samaniya ta ISS mallakar Rasha, da Amurka, da Canada, da tayyar Turai, da Japan, na daf da kammala aikin ta a shekarar 2024.

Idan har tashar ISS ta kawo karshen aikin ta kamar yadda aka yi hasashe, sabuwar tashar da kasar Sin ke fatan kaddamarwa a badi, za ta kasance daya tilo ke nan, kafin samar da wasu a nan gaba.

Baya ga wannan tasha, Sin da Rasha na fatan samar da wata tashar ta hadin gwiwar sassan biyu. Kafin nan a shekarar 2019, Sin ta kasance kasar farko a duniya, da ta aike da na’urar bincike, wadda ta sauka a bangare mai nisa na duniyar wata. Dukkanin wadannan matakai dai, na kara bayyana kudurin Sin na ci gaba da bunkasa ayyukan binciken sararin samaniya, da raya ilimin kimiyya, da nazari kan sauran duniyoyi dake wajen duniyar bil adama.

Ko shakka babu, harba wannan bangare na tashar binciken sararin samaniya na Tianhe, ya zamo muhimmin ci gaba, ga burin kasar Sin na zurfafa ayyukan sama jannati, wanda duniya baki daya za ta ci gajiyarsa. (Saminu Hassan)