logo

HAUSA

MDD ta ce ana samun karuwar rashin tsaro a yankin Sahel

2021-04-29 10:06:08 CRI

MDD ta ce ana samun karuwar rashin tsaro a yankin Sahel_fororder_0429-ahmad-1

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD ta ce, karuwa rikice-rikice, da karancin abinci, gami da annobar COVID-19 suna haifar da karuwar yunwa, da raba mutane da gidajensu a yankin Sahel, lamarin da ya shafi mutane kusan miliyan 29.

Ofishin jin kai na MDD (OCHA) ya ce, yanayin bukatar jin kai yana kara tsananta a shiyyar, inda aka yi kiyasin kusan mutane miliyan 29 za su bukaci tallafi da neman kariya a wannan shekara, adadin ya karu da miliyan 5 bisa na shekarar 2020.

Hukumar OCHA ta ce, daga shekarar 2015 zuwa 2020, hare haren da aka kaddamar ya ninka har sau takwas a tsakiyar Sahel, kana ya ninka sau uku a yankin tafkin Chadi.

A cewar hukumar jin kan, a yankin tafkin Chadi kadai, mutane miliyan 6.2 suna fuskantar matsalar yunwa a wannan shekara, inda aka samu karin kusan mutane miliyan biyu sama da na shekarar bara. A yankin tsakiyar Sahel wanda ya kunshi kasashen Mali, Burkina Faso da Nijer, mutane miliyan 3.4 na fuskantar matsalar abinci a cikin wannan shekara ta 2021, wanda ya kai matakin koli.

Hukumar tana neman dala biliyan 3.7 domin shirya ayyukan tallafin jin kai a kasashen Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Mali, Nijer da Najeriya.(Ahmad)

Bello