logo

HAUSA

Rancen Kudi Da Sin Take Baiwa Najeriya zai Amfani Juna Da Cin Moriya Tare

2021-04-28 16:45:19 CRI

Rancen Kudi Da Sin Take Baiwa Najeriya zai Amfani Juna Da Cin Moriya Tare_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20181219_180f8b917deb452c9fbaa8749b4524a5.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Daga Amina Xu

Kwanan baya, jaridar “The Sun” da ake wallafawa a Najeriya, ta ba da labari cewa, jama’ar kasar na nuna damuwa matuka kan rancen kudin da kasar take karba daga kasashen ketare, musamman ma kasar Sin, saboda a ganinsu irin wannan rancen kudi na da sharuda masu tsauri, idan kasar ta kasa biyan rancen, ya zama tilas ta mika ikon mulkinta hannun kasar Sin. Ita ma jaridar “The Guardian” ta wallafa wani labari cewa, shugaban hukumar gyare-gyare da raya kasa ta Najeriya Adekunle Ahmed ya kalubalanci gwamnati da ta sake kimanta rancen kudin da Sin ta baiwa kasar.

Bayan da na karanta rahotanni, a ganina, ya yiwu wasu ‘yan siyasa na Nijeriya ba su san yarjejeniyoyin basusuka da kasarsu ta kulla sosai ba.

Na farko, ana damuwa ne a sakamakon yadda ba a san ka’idar “ikon kasa na samun kariya daga shari’a”. A game da alakar ikon mulkin kasa da rancen kudi, darektan cibiyar yada labarai tsakanin Afrika da Sin, Ikenna Emuwu, ya taba wallafa wani bayani mai taken "Ikon mulkin Najeriya da rancen kudi da Sin ke bin kasar", inda ya ce, Sin ta baiwa kasar rancen kudi bisa ka'idar kasa da kasa, kuma bai keta ikon mulkin kasar ba ko kadan. Bayanin ya ce, wasu 'yan Najeriya sun aza ayar tambaya kan rancen kudin da Sin take bin Najeriya, a ganinsu wasu ayoyi daga cikinsu sun illata ikon mulkin kasar, amma wadannan ayoyi sun yi tanadin cewa, idan Najeriya ba za ta iya biyan kudin cikin lokaci ba, Sin za ta kai kara gaban kotu, kuma a matsayin Nijeriya na kasar dake da ikon mulki, ba za ta iya gudun doka da shari'a ba bisa ka’idar samun kariya daga shari’a. Babu shakka, duk wata kasa tana da ikon samun kariya daga shari’a, amma ba za a iya amfani da shi wajen harkokin kasuwanci ba. A shekarar 1977, wani kamfanin kasar Switzerland ma ya taba kai wa babban bankin Nijeriya kara, kuma a lokacin, kotun London ba ta yarda da baiwa babban bankin Nijeriya ikon kariya daga shari’a, har ma daga karshe an yanke hukunci a kan bankin. To, ta haka muna iya fahimta cewa, ayoyi na tabbatar wa kasar da ke bin rancen kudi ikon kai kara gaban kotu a yayin da kasar ke karbar kudin ya kasa biya, sam ba shi da alaka da batun lalata ikon mulkin kasa, balle ma maganar mika ikon mulkin kasa hannun wata.

A baya, ministan sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi ya shedawa manema labarai cewa, Sin ita ce kasa daya tilo a duniya dake samar da rancen kudi bisa dan kudin ruwa kadan da ya kai kaso 2.8% kawai, kuma babu wata kasar da za ta samar da rancen kudi ga wata amma ba tare da tabbatar da tsaron kudin ba? wadannan rancen kudi ba mu ne muka karba ba, masu aiwatar da ayyuka sun ne za su karbi kudin. Idan sun kammala aiki za a biya su. An riga an tabbatar da wasu ayyuka, shin ko ana son shafa wa  aikin layin dogo da aka gina tsakanin Abuja da Kaduna bakin fenti?

A hakika, layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna ya kyautata yanayin zirga-zirga a kasar, wanda ya raya tattalin arziki da jin dadin al’ummar kasar sosai, ban da wannan kuma ya samar da dimbin guraben aikin yi.

Wani fasinja da ya kan bi wannan layin dogo mai suna Babatunde Lawal ya ce, “wannan layin dogo ya rage tsawon lokacin zirga-zirga dake tsakanin wadannan birane biyu, wanda ya samar sauki gare mu. Ban da wannan kuma, ya samar da dimbin guraben aikin yi.”

Ban da haka, jirgin kasa mai saurin tafiya dake cikin birnin Abuja ya taba fuskantar kalubale na karancin kudade, abin da ya kai ga dakatar da wannan aiki, sai dai daga baya rancen kudi daga kasar Sin ya taimaka wajen farfado da wannan aiki. Anthony Agwaniru injiniya dake kula wannan aiki ya ce, “Bankin shigi da fici na kasar Sin ya ba da rancen kudi mai gatanci a shekarar 2012, saboda haka, an farfadowa da aikin a watan Jarairu na shekarar 2013. Wannan aiki da samar da dubban guraben aikin yi, ya kuma baiwa kanana da matsakaitan kamfanonin wurin damar bude kofarsu, ta yadda Abuja zai samun karin kudin shiga.”

A game da batun rancen kudi, shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, “Najeriya ta kulla huldar abota da Sin karkashin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika, matakin da ya taimakawa kasar ingiza karfinta na gina manyan ababen more rayuwa a duk fadin kasar. Wadannan ayyuka da aka yi a shekarun baya-bayan nan ya dace da shirin farfado da tattalin arzikin kasa da gwamnatinmu ke aiwatarwa, hakan ya sa muna da cikakken karfin biyan rancen kudin da muka karba.”. Gaskiyar magana shi ne, neman rancen kudi hanya ce ta samun bunkasuwa na dogon lokaci, amma idan an nuna shakku kan huldar Sin da Najeriya har ake adawa da rancen kudin da Sin take baiwa kasar bisa karairayi da wasu suke yadawa, wannan rashin wayewa ne. Wasu ‘yan siyasa dake baza jita-jita wai rancen kudin da Sin take baiwa Najeriya tarkon bashi ne, su ‘yan amshin shatan wasu kasashen yamma ne, su manta da zamantakewar jama’ar kasar inda suke zama a inuwa guda wajen shafawa kasar Sin bakin fenti. (Amina Xu)