logo

HAUSA

Kokarin kasashen duniya na ganin bayan cutar malaria

2021-04-28 10:57:41 CRI

Gwajin alluran riga kafin cutar zazzabin cizon sauri ko Malaria, da aka yi wanda jami’ar Oxford ta samar, ya nuna cewa, akwai fata mai kyau game da kokarin da ake yi na ganin bayan daya daga cikin manyan cututtukan dake halaka rayukan jama’a musamman yara da mata masu juna biyu a duniya.

Kokarin kasashen duniya na ganin bayan cutar malaria_fororder_210428-世界21015-hoto3

Allurar riga kafin wanda jami’ar ta Oxford ta samar mai suna R21, ta kuma nuna ingancin kaso 77 cikin 100 a gwajin da aka yiwa yara 450 a kasar Burkina-Faso cikin watanni sha biyun da suka gabara. Wannan shi ne karo na farko da aka cimma burin taswirar WHO game da yaki da wnnan cuta dake da ingancin a kalla kaso 75 cikin 100. Haka kuma, wannan sakamako ya kasance mai faranta rai a riga kafin dake mataki na gwaji.

An kasa yaran guda 450 dake tsakanin watannin 17 zuwa shekaru 5 cikin rukunnai uku. Kuma bincike ya nuna cewa, babu wata illa da aka gano a cikin riga kafin.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yaba dukkan kasashen da suka yi nasarar cimma burinsu na ganin bayan cutar zazzabin cizon sauro ko malaria a kasashensu.Yana mai cewa, hakan yana nunawa duniya cewa, za a iya ganin bayan cutar ta Malaria.

Kokarin kasashen duniya na ganin bayan cutar malaria_fororder_210428-世界21015-hoto2

Daga shekarar 2000 zuwa 2019, yawan kasashen da ake samun kasa da mutane 100 masu fama da wannan cuta, ya karu daga shida zuwa kasashe 27, inda ya yi misali da alkaluman hukumar lafiya ta duniya dake nuna cewa, an kusa ganin bayan cutar. Sai dai hanya daya ta cimma wannan nasara, ita ce samar da kudade, da tsare-tsaren sanya ido da shigar da al’umma cikin wannan aiki.

Bayanai na nuna cewa, sama da mutane 400,000 ne cutar take hallakawa a kowace shekara, galibinsu kananan yara a yankin Afirka, baya ga sabbin mutane sama da miliyan 200 da cutar ke kamawa a kowace shekara.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, a shekarar 2019, nahiyar Afirka ce, ke da kaso 94 cikin 100 na wadanda cutar ta kama da ma kisa a duniya baki daya, kuma sama da wannan adadi suna kasashe biyar ne, da suka hada da Najeriya mai kaso 27, sai Jamhuriyar demokiradiyar Congo dake da kaso 12, Uganda da Nijar na da kaso biyar kowanne, yayin da kasar Mozambique ke da kaso 4 cikin 100. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)