logo

HAUSA

Wei Zhenling: ‘Yan kabilar Maonan sun fara jin dadin zaman rayuwarsu sakamakon fita daga kangin talauci

2021-04-27 14:58:53 CRI

Wei Zhenling: ‘Yan kabilar Maonan sun fara jin dadin zaman rayuwarsu sakamakon fita daga kangin talauci

A ko wace shekara, Wei Zhenling kan yi bulaguro zuwa garinsu dake yankin Guangxi na kabilar Zhuang mai cin gashin kai da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Sai dai, a ganin Wei da yayanta da ‘yar uwarta da iyayenta, wadannan tafiye-tafiye na da matukar wahala.

Inda suka nufa, gari ne na al’ummar kabilar Maonan, wanda ke can cikin jerin tsaunuka a gundumar Huanjiang ta kabilar Maonan mai cin gashin kanta.

Domin tabbatar da sun isa kafin dare, iyayensu kan tada su daga barci tun da sanyin safiya, domin su yi sammako su samu jirgin kasa na farko da zai je yankin.

Sai kuma mataki mafi wahala na tafiyar.

Mataki na karshe na tafiyar ya kunshi tafiyar kafa ta tsawon sa’o’i 5 a kan duwatsu, ga kuma nauyin tsarabar da suka dauko domin ‘yan uwa da abokan arziki da suka dade ba su gani ba.

Tafiya a hankali, kan tituna masu duwatsu ya kusan zama tarnaki ga burin Wei na fahimtar al’adunta.

Wei, babbar mai shigar da kara daga Guangxi, ta ce “sabo da al’adar da kewar gida ne ke rike ni yayin wadancan tafiye-tafiye”.

Wei, ita kadai ce ‘yar kabilar Maonan dake cikin majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wadda ta gudanar da taro a farkon watan Maris a Beijing, a lokaci guda da majalisar wakilan jama’ar kasar Sin dake zaman majalisar dokokin kasar.

A bara ne al’ummar kabilar Maonan 107,000, da galibinsu ke zaune a gundumar Huanjiang mai zaman kanta dake kusa da lardin Guizhou, suka yi adabo da talauci, a yayin da JKS ke burin kawar da taluci a baki dayan kasar, kafin bikin cikarta shekaru 100 da kafuwa a bana.

Wei ta ce nisan yankin ya kara talaucin da mutane suka fuskanta zuri’a bayan zuri’a.

Yayin da suke bulaguro, mahaifin Wei, dan kabilar Maonan da ya zama malamin ilmin aikin kira da lissafi bayan kammala kwalejin horar da malamai ta yankinsu, ya bada labarin yadda yake bin wannan hanyar sau 1 a ko wane zangon karatu domin zuwa makaranta daya tilo dake yankin.

Wei ta ce, “babana ya ce idan ya hango garin daga saman tsauni, sai ya fashe da kuka.”

Ta kara da cewa, ba ta ji dadi ba da ta samu labarin cewa, yana wuya galibin al’ummar Maonan da suka bar yankin, su je ganin gida, balle ma a ce su koma.

Nisan yankin ne ya haifar da matsalar, sannan ya taimaka wajen rashin sauya tunani, abun da ke tilastawa al’ummar rungumar tsohon tsarin rayuwa.

“kudi ba shi da amfani a nan, tsarin ba ni gishiri in ba kamanda ake amfani da shi don samun abubuwan bukatun yau da kullum,” cewar Wei.

Innarta, ‘yar kabilar Maonan, na kiwon dabbobi don musaya, sannan ta kan adana isasshen shinkafa da hatsin da take bukata na amfani.

Mahaifiyar Wei, ‘yar kabilar Han, wadda ke fahimtar harshen Maonan amma ba ta iya magana da shi ba, na dogaro ne da mijinta, domin ya yi musaya ya samo kayayyakin bukata a cikin kauyen. Mamanta ta ce, ta yi ta kokarin sayar da abubuwa amma ba wanda zai sayi abu daga bako.

Wei da ta saba da rayuwar birni, kan kwana ne rumfa guda da dabbobi. Sai dai abun da ya fi damunta shi ne warin dake tashi a wurin.

Wei Zhenling: ‘Yan kabilar Maonan sun fara jin dadin zaman rayuwarsu sakamakon fita daga kangin talauci

A kauyen, ruwa abu ne mai matukar daraja, musammam a lokacin rani da hunturu. “Mamana kan ce mu ba ko wane digon ruwa daraja”, a cewar Wei.

Ruwan da iyalan ke wanke fuskarsu da shi, shi ne ake ajiyewa a wanke hannu da shi, kafin daga bisani a ba dabbobi.

A irin wannan yankin mai duwatsu, mai koguna kalilan, sai an haka mitoci da dama kafin a samu ruwa.

Mutanen sun dogara ne da ruwan sama dake taruwa a wani kududdufi dake kusa da kauyen a matsayin hanyar samun ruwa. A cewar Wei, babu zance tsafta, shi ya sa ake samun matuwar jarirai sosai.

Baya ga haka, kududdufin kan bushe a lokacin hunturu, lokacin da babu ruwan sama, lamarin dake tilastawa mutanen tafiya wani kauye domin neman ruwa.

Wahalar da ake sha na neman ruwa ne ya sa kakan Wei, wanda shi ne dagacin kauyen a lokacin, ya kaddamar da aikin hakar duwatsu domin neman ruwa daga karkashin kasa.

Daga bisani, an samu ruwan, sai dai kakan nata ya rasa idonsa daya yayin aikin.

Wei ta ce, “da na sauka daga matakalar duwatsu a cikin wannan rami mai duhu, gomman mitoci a karkashin kasa, na ji tsoron zai iya rushewa a kowane lokaci.”

Noman rani ba abu ne mai yuwuwa ba, don haka mutanen kauyen ba su da wani zabi sai dai noman masara da waken soya, wadanda za su iya jure fari, sai dai kuma bukatun dole kadai suke iya biya.

A bara, hukumomi suka sanar da ficewar Huanjiang daga kangin talauci, kuma a yanzu, kowanne iyali na samun ruwan famfo.

A kauyensu Wei, wanda mazauni ne na dubban mutanen kabilar Maonan, ana samun ruwan famfo ne daga tuka-tukar da aka samar daga rijiyoyin da hukumomin yankin suka haka.

Huang Bingfeng, shugaban gundumar kuma dan kabilar Maonan, ya ce a wani yankin dake kusa da su mai mazauna 20,000 ‘yan kabilar Maonan, hukumomi sun gina wata hanyar ruwa domin karkata akalarsa daga wani kogi mai nisan kilomita 12 daga yankin, da nufin samarwa al’umma ruwa.

An gina tituna yanzu, a wani bangare na shirin samar da ababen more rayuwa a yankunan karkara.

Karin hanyoyi da magudanar ruwa, ya ba mutane damar noman shinkafa da itatuwan mulberry da Pamelo. A sanadin haka, wasu mazauna sun fara aikin sufuri, yayin da wasu suka karbi tallafin gwamnati na kiwon dabbobi, wanda ke samar da kudin shiga, cewar Wei.

Al’ummar Maonan na daga cikin kananan kabilu 28 na kasar Sin da suka fita daga kangin talauci, zuwa watan Nuwamban bara.

Wei ta ce, “kakannina sun mutu, don haka ba mu cika zuwa gida ba yanzu. Idan mun je, to mun je ne domin bikin share kaburbura, yanzu da mota muke zuwa tsohon gidanmu”.

Kande