logo

HAUSA

Binciken masana: Sinawa na nuna gamsuwa da salon gwamnatin kasar Sin

2021-04-27 17:12:21 CRI

Binciken masana: Sinawa na nuna gamsuwa da salon gwamnatin kasar Sin_fororder_微信图片_20210427171005

Masu hikimar magana na cewa “labarin zuciya a tambayi fuska.” A wani kaulin kuma, “na ji dadi shi ne gari ba nasaba ba.” Sakamakon wani rahoton binciken masana ya gano cewa al’ummar Sinawa suna matukar gamsuwa da salon shugaban kasar Sin. Alkaluman rahoton ya nuna cewa, kashi 93.1 cikin dari na jama’ar kasar Sin sun nuna gamsuwa ga gwamnatin kasar a shekarar 2016. A watan Yulin shekarar bara, cibiyar Ash mai kula da tafiyar da harkoki ta hanyar demokuradiyya da kirkire-kirkire na kwalejin gwamnatin Kennedy na jami’ar Harvard ta gabatar da wani rahoto mai taken “fahimtar karfin jam’iyyar kwaminis ta Sin ta hanyar yin binciken ra’ayoyin jama’ar Sin a dogon lokaci.” Kwararru uku na kwalejin sun yi bincike sau 8 a kasar Sin tun daga shekarar 2003 zuwa 2016, inda suka yi hira fuska da fuska da jama’ar kasar Sin daga birane da kauyuka fiye da dubu 30, sannan suka rubuta wannan rahoto. Bisa rahoton, tun daga shekarar 2003, jama’ar kasar Sin sun kara nuna gamsuwa ga gwamnatin kasar Sin. A cikinsu, jama’a daga yankunan dake tsakiyar kasar da kuma yankuna masu fama da talauci sun fi kara nuna gamsuwa ga gwamnatin kasar. Masanin Sudan ya ce, jam’iyyar CPC tana da kwarewar shugabanci. Hakika idan Sinawa sun bayyana hakan za mu iya cewa bai zo da mamaki ba, domin an ce gani ya kori ji, kuma ruwan da ya jika ka shi ne ruwa. Ko da yake, ba kawai al’ummar Sinawa ne kadai ke da irin wannan ra’ayi ba, a kwanakin baya ma, wani kwararren masanin siyasar kasar Sudan ya bayyana kwarin gwiwa game da kwarewar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC ke da shi wajen cigaba da inganta tsarin shugabanci bisa amfani da salon kwarewar da take da shi, jam’iyyar ta cimma manyan nasarorin bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma, kana ta kyautata yin sauye-sauye da bude kofa. Abdul-Khaliq Mahjoub, wani shehun malami ne a fannin siyasa a cibiyar nazarin kimiyyar siyasa dake Khartoum, ya ce shekarar 2021 ta yi daidai da cika shekaru 100 da kafuwar JKS, kuma ya kasance wani muhimmin lokaci bisa lura da irin rawar da jam’iyyar ta taka, ba wai ga kasar Sin kawai ba har ma ga duniya baki daya. A cewarsa, a cikin shekaru 100 da suka gabata, jam’iyyar CPC ta yi nasarar jagorantar kasar Sin wajen kaiwa matakai daban daban na ci gaba da samun makoma mai haske ta hanyar wasu ingantattaun tsare-tsare masu alfanu. Mahjoub ya bayyana kwarewar da jam’iyyar CPC ta nuna a yaki da annobar COVID-19 a matsayin wata hujja dake kara tabbatar da karfin da jam’iyyar ke da shi wajen tinkarar manyan batutuwa. Tun bayan barkewar annobar, jam’iyyar ta yi ta kokarin zaburar da rassanta dake yankunan kasar domin taimakawa shirin dakile annobar da kuma karfafawa Sinawa gwiwa don kawar da annobar COVID-19," in ji masanin. (Ahmad Fagam)