logo

HAUSA

Gwamnatin Sin za ta dauka matakai 28 domin gina yankin cinikayya maras shinge na Hainan

2021-04-27 12:39:30 CRI

Gwamnatin Sin za ta dauka matakai 28 domin gina yankin cinikayya maras shinge na Hainan_fororder_hainan

Jiya Litinin 26 ga wata, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata sanarwa game da daukar matakai a jere domin ingiza gina yankin cinikayya maras shinge da aka kafa a tsibirin Hainan dake kudancin kasar, inda aka sanar da cewa, za a dauki matakai 28 domin kyautata ayyuka a fannonin cinikayyar kayayyaki da ta hidimomi.

A cikin sanarwar da aka fitar jiya, an bayyana cewa, za a saukaka iznin kara mai a jiragen ruwan dake jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa, da raya da goyon bayan aikin fitar da tsoffin motoci zuwa ketare, da kara goyon bayan sabon salon cinikayyar dake tsakanin kasa da kasa da sauransu, masanan da abin ya shafa sun nuna cewa, matakai 28 da za a dauka, za su ingiza cinikayya maras shinge a yankin Hainan, haka kuma za su saukaka cinikayya a tsibirin.

Jiya a nan birnin Beijing, shugaban hukumar kula da yankunan cinikayya marasa shinge ta ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, matakan da za a dauka suna da babbar ma’ana, saboda za su taka rawar gani kan ci gaban yankin cinikayya maras shinge na Hainan, a cikin wadannan matakai, akwai matakai sha uku da za su saukaka cinikayyar kayayyaki, sauran guda sha biyar kuwa, za su saukaka cinikayyar hidimomi, Tang Wenhong yana mai cewa,“Alal misali, a yankin raya tattalin arziki na Yangpu dake tsibirin, za a fara yin gwajin shigowa ko fitar da danyen mai ko man da aka tace ta hukumar kwastam kai tsaye, wato babu bukatar nuna shaidar iznin kamfani ko kuma kayyade yawansu ba, kana ba za a kara harajin sukarin da za a shigo da su kasar Sin daga ketare ba, duk da cewa adadin zai zarce kwatankwacin adadin da aka tsara, ban da haka kuma, idan akwai bukata, za a gabatar da alkaluman kayayyaki ga hukumar kwastam domin hukumar ta tantance su. Duk wadannan matakai za su kyautata aikin hukumar kwastam ta tsiribin Hainan a nan gaba.”

Gwamnatin Sin za ta dauka matakai 28 domin gina yankin cinikayya maras shinge na Hainan_fororder_4

A shekarar bara da ta gabata, babban shirin gina yankin cinikayya maras shinge na Hainan ya tabbatar da cewa, za a gina yankin musamman na jigilar kayayyakin da ake shigo da su daga ketare a fadin tsibirin Hainan karkashin sa idon hukumomin da abin ya shafa, wato ana iya shigo da kayayyaki tsibirin Hainan daga sauran kasashe kai tsaye, ban da wasu kayayyakin da gwamnatin kasar Sin ta hana ko kayyade shigo da su kasar, a sa’i daya kuma, idan za a yi jigilar kayayyakin zuwa sauran sassan kasar, to, za a kara karfafa aikin tantance su bisa ka’idojin da abin ya shafa, haka kuma za a biya haraji bisa ka’ida, ana sa ran cewa, za a kammala aikin share fage kafin shekarar 2025, kuma za a kaddamar da aikin jigilar kayayyakin da ake shigo da su daga ketare a fadin tsibirin Hainan a shekarar 2025.

Tang Wenhong ya kara da cewa, sabbin matakai 28 da za a dauka, za su mai da hankali kan aikin yawon shakatawa, da sana’ar samar da hidima ta zamani, da kuma sana’o’in fasahohin zamani, a cewarsa:“Gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan lardin Hainan domin ya raya sabon salon cinikayyar kasa da kasa, da cinikayya ta yanar gizo, da cinikayyar fasahohi, da ta al’adu, da gina cibiyar baje kolin kasa da kasa, da gina sansanin fitar da al’adun kasa, da gina sansanin cinikayyar al’adu ga ketare na kasar, haka kuma tana sa kaimi kan sabon salon hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin cinikayyar hidimomi, ta yadda za a kafa sana’o’in dake nuna fifiko masu siffar musamman na lardin Hainan, tare kuma da kyautata muhallin kasuwanci a tsibirin.”

A nasa bangare, mataimakin babban sakataren gwamnatin lardin Hainan Sun Shiwen ya yi bayani cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata, lardin Hainan ya dukufa domin ingiza kwaskwarimar cinikayya, kuma ya yi kokari matuka wajen samun ci gaban cinikayya mai inganci a lardin, haka kuma ya samu babban sakamako wato cinikayyar waje a lardin ta karu a kai a kai, har karuwar adadin kayayyakin da ake shigo da su kasar daga ketare ba tare da biyan haraji ba ta kai kaso 260 cikin dari, yankin raya tattalin arziki na Yangpu a tsibirin shi ma ya jawo hankalin masu zuba jari matuka, kawo yanzu gaba daya kamfanonin ketare da yawansu ya kai 425 da suka zo daga kasashe 33 sun shiga yankin na Yangpu, mataimakin babban sakataren gwamnatin lardin Hainan Sun Shiwen ya kara da cewa,“Nan gaba lardin Haina zai kara karfafa cinikayya dake tsakaninsa da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, da sauran kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, kuma zai kyautata tsarin tabbatar da cinikayya domin samun ci gaba mai inganci.”(Jamila)