logo

HAUSA

Manufar bautawa jama’a ta sa kasar Sin cimma burin kawar da talauci

2021-04-26 08:31:13 CRI

Bankin duniya ya gabatar da wani rahoto a watan Oktoban bara cewa, sakamakon annobar COVID-19, da rikice-rikice, da dumamar yanayin duniya, yawan mutane masu fama da tsananin talauci (wadanda kudin shigarsu a kowace rana ya yi kasa da dalar Amurka 1.9) ya sake karuwa a duniya. Inda aka yi hasashen cewa, yawan mutanen da suke fama da tsananin talauci ka iya kaiwa miliyan 150 a bana. Sai dai a kasar Sin, ana cikin wani yanayi na daban.

Kasar Sin ta fara aiwatar da wasu matakai na musamman na kawar da talauci a shekarar 2012. Zuwa ranar 25 ga watan Fabrairun bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar cewa, kasar ta cimma nasarar kawar da talauci baki daya daga cikin gidanta.

Kafofin watsa labaru na kasashe daban daban sun watsa labarai game da wannan babban ci gaban da kasar Sin ta samu, tare da gabatar da tambaya iri daya: Ta yaya kasar Sin ta samu nasarar kawar da talauci, a matsayinta na wata kasa dake kan hanyar tasowa, wadda yawan al’ummarta ya kai biliyan 1.4?

Hakika dai a matsayina na Basine, ban yi mamaki ba bisa nasarar da kasata ta samu a kokarinta na kawar da talauci. Saboda tun tuni na saba da ganin yadda ake kokarin aiwatar da manufofin tallafawa mutane marasa karfi.

A unguwar Cao Qiao dake kudancin birnin Beijing na kasar Sin, akwai wata cibiyar taimakawa mutane marasa karfi ta hanyar kasuwanci, inda ake samun dimbin rumfuna masu sayar da kayayyakin yankuna masu fama da koma bayan tattalin arziki, irinsu abinci, da kayayyakin hannu, da na masarufi, da dai sauransu. A kan samu masu sayen kaya da yawa a cibiyar, wadanda suke samar da karin kudin shiga ga masu samar da kayayyakin, bisa duk wani kayan da suka saya. Wani ma’aikaci mai kula da rumfar wani kamfanin dake cikin cibiyar kasuwancin ya gaya mana cewa, kamfaninsu ya kulla huldar hadin gwiwa tare da wasu yankuna marasa ci gaban tattalin arziki na lardin Qinghai dake yammacin kasar Sin, inda suke sayen shanun da manoman wurin suka kiwata, da sarrafa naman zuwa kilishi, sa’an nan suna sayar da kilishin a wasu manyan biranen kasar Sin. Ta wannan hanya, manoman ba za su sake gamuwa da matsala a fannin sayar da shanunsu ba.

Sa’an nan, a yankin Miyun dake karkarar binin Beijing, ana samun duwatsu da yawa, batun da ya kawo cikas ga aikin noma, tare da haddasa koma bayan tattalin arziki. Sai dai yanzu a wurin na ga yadda wasu kamfanoni ke koya wa manoma fasahar kiwon kudan zuma, domin su shiga ayyukan hada ruwan zuma. Ta wannan hanya, ana samun kare muhalli na wurin, gami da baiwa manoman damar samun karin kudin shiga.

Manufar bautawa jama’a ta sa kasar Sin cimma burin kawar da talauci_fororder_0426-1

Yayin da ake kokarin aiwatar da manufar kawar da talauci a kasar Sin, ko mutane masu karamin karfi ma suna samun cikakkun damammakin raya kai, da wadatar da kai. Na taba hira da wani saurayi mai suna Chen Zifang, wanda ke zama a gundumar Badong ta lardin Hubei. An haife shi ba shi da hannaye, don haka ya sha dimbin wahalhalu kafin ya girma. Amma yanzu ya samu damar sayar da kayayyakin kauyensu zuwa wurare daban daban, ta hanyar watsa bidiyo da sayar da kaya ta yanar gizo ta Internet, inda ya ba da taimako a kokarin fidda magidanta fiye da 200 daga kangin talauci.

Manufar bautawa jama’a ta sa kasar Sin cimma burin kawar da talauci_fororder_0426-2

Idan mutum na zaune a kasar Sin, zai ga kayayyaki da yawa, da sauraron labarai iri-iri, masu alaka da aikin kawar da talauci. Kana baya ga wadannan abubuwa, zai iya ganin yadda gwamnatin kasar take ba da taimako. Gwamnati ce ta bada umarnin kulla huldar hadin gwiwa tsakanin kamfanoni da manoma, da yayata dabarar tallafawa mutane marasa karfi ta hanyar sayen kayayyakin da suke samarwa, da taimakawa mutane irin Chen Zifang samun damar raya kansu. Sai dai dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta iya daukar wadannan nagartattun matakai shi ne, domin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) dake kan ragamar mulkin kasar tana da wata babbar manufa daga tushe, wadda ita ce “A yi iyakacin kokarin bautawa jama’a.”

Idan ka yi nazari kan tarihin kasar Sin, da yanayin da kasar ke ciki yanzu, za ka fahimta cewa, ko a lokacin da JKS ke kokarin neman ‘yantar da jama’ar kasar, ko a lokacin da take neman raya tattalin arziki da masana’antu a kasar, ko a lokacin da take neman tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, ko kuma yayin da jam’iyyar ke daukar matakan tinkarar annobar COVID-19, JKS sam ba ta taba kaucewa babbar manufarta ba, inda take ta kokarin nemo wa jama’ar kasar dimbin alfanu. Ma iya cewa, ainihin dalilin da ya sa kasar Sin samun ci gaban tattalin arzikinta cikin sauri matuka shi ne, domin JKS ta cika alkawarinta, inda ta yi kokarin raya kasa ne domin jama’ar ta, da dogaro kan jama’a a kokarin tabbatar da ci gaban kasa, gami da sanya dukkan jama’ar kasar jin dadin sakamakon da aka samu.

Charles Onunaiju, shi ne darektan cibiyar nazarin kasar Sin ta kasar Najeriya. Ya taba rubutawa a cikin wani bayaninsa cewa, a karkashin jagorancin JKS ne, kasar Sin ta samu damar raya tattalin arzikinta cikin matukar sauri, don haka ya bukaci jam’iyyun kasashen Afirka da su yi koyi da JKS a fannin gudanar da mulki. A ganina, wata babbar manufar JKS a fannin aikin mulki ita ce “Kokarin bautawa jama’a”. Idan wata jam’iyya za ta iya gudanar da wannan manufa, to, za a fara samun wani nagartaccen mulki. (Bello Wang)

Bello