Ga yadda 'yan sandan ko ta kwana na lardin Guangdong suke begen karnukn tsaro da suka rasu
2021-04-26 08:54:22 CRI
A kan wani dutsen dake kusa da sansanin ’yan sandan ko ta kwana na lardin Guangdong, an kebe wani fili, inda aka binne karnukan tsaro guda 20. A “Ranar Tsabtace Kabari”, wato wajen ranar 4 ga watan Afrilun kowace shekara, ’yan sandan ko ta kwana dake wannan sansani, su kan tafi can tare da karnukan su, domin tunawa da karnukan tsaro da suka rasu. (Sanusi Chen)