logo

HAUSA

Raba alluran rigakafi cikin yanayin rashin adalci na halaka rayukan al’umma

2021-04-26 16:09:36 CRI

Raba alluran rigakafi cikin yanayin rashin adalci na halaka rayukan al’umma_fororder_210426-sharhi-maryam-hoto

Cikin kwanaki 4 da suka gabata, a ko wace rana, adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar Indiya na zarce dubu dari 3, kuma kasar na fama da karancin magani da alluran rigakafi. Baya ga haka, gawarwaki sun kara yawa, har ya kai mutanen kasar na kone gawarwakin iyalansu da kansu. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, yanayin ya zama tamkar Wuta a cikin duniya.

Domin matsawa Amurka lamba da gamayyar kasa da kasa suka yi, a ranar 25 ga wata, kasar ta sanar da cewa, za ta samar da taimakon kayayyakin alluran rigakafi ga kasar Indiya. Amma, yadda Amurka ta dakatar da wannan aiki a baya, ya harzuka al’ummar Indiya.

A wannan lokaci, kasar Indiya ta fi bukatar alluran rigakafin cutar COVID-19 a maimakon kayayyakin sarrafa alluran. Shi ya sa, jaridar the Hindu ta fidda bayanin cewa, “abin takaici shi ne, Amurka ba ta ambaci ba da tallafin alluran rigakafi kai tsaye ga kasar ba.”

Kwayar cutar tana ta yawo, yadda kasar Amurka take yi kuma, ya harzuka al’umma, a halin yanzu, raba alluran rigakafi cikin yanayin rashin aldaci ya hana hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar.

Kasar Indiya ita ce kasar da ta fi samar da alluran rigakafi bisa shirin COVAX da hukumar kiwon lafiyar duniya ta tsara, amma, tabarbarewar yanayi a cikin kasar, da hana fitar kayayyaki da kasar Amurka ta yi sun haifar da jan kafa ga aikin sarrafa alluran rigakafi. Kasashen dake matukar bukatar alluran rigakafin za su dade suna jira.

Shugaban kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross, Peter Maurer ya bayyana cewa, idan aka gaza raba alluran rigakafin cikin aldaci, annobar za ta kawo karin barazana ga kasa da kasa, kamar karin rikice-rikice, da karin masu fama da talauci. Wadanda ba sa raba alluran cikin adalci, za su haifarwa kan su matsala. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)