logo

HAUSA

Rancen kasar Sin na raya kasa ne ba wai tarko ba

2021-04-26 15:50:51 CRI

Rancen kasar Sin na raya kasa ne ba wai tarko ba_fororder_0426-01

Har yanzu ana ci gaba da cece kuce da fargaba game da irin rancen kudin da Sin take ba kasashe masu tasowa musammam kasashen Afrika, ciki har da Nigeria, inda ake ikirarin cewa kasar Sin na danawa kasashen tarkon bashi ko kuma neman yi musu mulkin mallaka idan suka gagara biya.

Gwamnatin kasar Sin ta sha jaddada cewa, rancen da take bayarwa ba na ayyuka marasa muhimmanci ba ne, burinta shi ne, kasashen nahiyar Afrika da ma sauran kasashe masu tasowa, su samu ci gaba kamar yadda ta samu, sannan su kyautatawa al’ummarsu. Don haka, dabara ta ragewa mai shiga rijiya! Lallai ya kamata gwamnatoci su san yadda za su juya rancen ta hanyar da zai yi alfanu ga ci gabansu da al’ummominsu, sannan su yi amfani da shi wajen samar da hanyoyin samun kudaden da za su kai ga biyan rancen har ma da samun dimbin riba.

Idan ana kokawa da rashin kudi a matsayin dalilin da ya sa ake fuskantar koma baya tattalin arziki da na kayayyakin more rayuwa a kasashen Afrika, to kasar Sin ta kawo dauki, saura gwamnatoci su yi namijin kokarin yin abun da ya dace, ba wai barin kudaden su zurare ba.

Akwai sharudda da ake dubawa kafin bayar da bashi. Dole ne mai bayar da bashin ya duba karfin kasar da za a ba rancen don tantance ko za ta iya biya ko kuma a’a. Kana ita ma mai karbar bashi, dole ne ta san cewa tana da karfin biya ko kuma a’a. Don haka, kafin ma a bayar da bashin, sai kowanne bangaren ya tabbatar da cewa za a iya biya.

A zahiri ba badini ba, za a iya ganin dimbin ayyukan da kasar Sin ta yi a Nijeriya, kama daga layukan dogo zuwa gyaran filayen jiragen sama da tituna da sauransu, duk cikinsu babu na banza sai ma na san barka. Ko a tattaunawar da ta yi da sashen Hausa na rediyon kasar Sin, a ranar 26 ga watan Afrilun 2019, yau shekara 2 cif da suka gabata, ministar kudin Nigeria, Zainab Ahmed, ta karyata cewa kasar Sin na dama musu tarkon bashi, tana mai cewa wajibi ne kan kowacce kasa dake neman aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa ta nemi bashi, don haka suke karbar rance daga kasar Sin bisa la’akari da cewa nata na da rangwamen kudin ruwa da saukin biya. Ta kara da cewa a matsayinsu na kasashe masu tasowa, suna bukatar taimako daga manyan kasashe irin kasar Sin, kuma dangantakar kasashen biyu ta moriyar juna ce, domin kamfanonin kasar Sin da ke aiki a kasar, na daukar ma’aikata ’yan kasa tare da horar da su. Wato wannan na nufin Nijeriya da ma sauran kasashen Afrika na harbin tsuntsaye biyu da dutse 1.

Bugu da kari, kowa yana neman inda zai samu sauki. A halin da ake ciki na matsi, wa zai nemi karawa kansa matsi? Dole ne kasashen su karkata ga inda za su samu gata, da sauki da biyan bukata cikin lumana ba tare da sanya kansu cikin tasku ba.

Tun farko, kasashen yamma ne suka fara ikirarin cewa, kasar Sin na danawa kasashen Afrika tarkon bashi, inda wannan zance ya fara darsuwa a zukatan jama’a. Amma abun tambaya a nan shi ne, su da me suka amfanawa kasashen na Afrika? Har gobe basussukan Turai da Amurka, ba su da saukin karba, duk kuwa da dimbin moriyar da suka samu a nahiyar. Burinsu na fara wannan yada wadannan zantuka marasa tushe shi ne, neman dakushe tasiri da farin jinin da kasar Sin ke da shi a nahiyar Afrika.

Zancen cewa gazawa wajen biyan bashi zai kai Sin ga kwace iko da kasashe ma bai taso ba. Domin ta sha nanata cewa, ba ta da niyya, kuma ba za ta taba neman fadada ikonta ko yin babakere ko danniya ba. Haka kuma ba za ta taba neman ci gaba ta hanyar gargajiya da manyan kasashe suka bi ba. Kasar Sin ba ta yi mulkin mallaka ba. Kuma zuwa yanzu, ta kai matsayin da kasashen da suka yi mulkin mallakar suka kai, amma ta hanyar amfani da albarkatun da take da su a cikin gida da kuma zabarwa kanta hanyar da take ganin ya dace da ita da kuma al’ummarta. Don haka, tana da hanya mafi sauki na samun ci gaba da karfi, ba tare da fadada ikonta, ko da na tarko ba. (Faeza Mustapha)