logo

HAUSA

Cinikayyar amfanin gona tsakanin Sin da Afirka ta samu damar neman karin ci gaba

2021-04-25 17:15:19 CRI

Cinikayyar amfanin gona tsakanin Sin da Afirka ta samu damar neman karin ci gaba_fororder_210425-sharhi-Sanusi-hoto

A ’yan kwanakin baya, ba gaira ba dalili, gwamnatin kasar Australiya ta ki amincewa da yarjejeniyar hadin gwiwa bisa shawarar “Ziri daya da Hanya daya” wadda jihar Victoria ta kasar Australia da bangaren Sin suka kulla. Kasar Australiya tana kawance da kasar Amurka wadda take daukar matakai daban daban na hana bunkasuwar kasar Sin. Sabo da haka, ba mu yi mamakin matakin da gwamnatin Australiya ta dauka ba. Yanzu kasar Australiya ba ta son yin mu’amala da kasar Sin kamar yadda ya kamata ba. Hakan ya sa, kasar Sin ba za ta karfafa dangantakar dake tsakaninta da kasar Australiya ba, kuma ba za ta ci gaba da sayen wasu kayayyaki daga kasar Australiya ba. Sakamakon haka, a ganina, yanzu kokarin zurfafa huldar cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka shi ne a gabanmu, musamman a fannin cinikin amfanin gona. Ma iya cewa, Cinikayyar amfanin gona tsakanin Sin da Afirka ta samu damar neman karin ci gaba.

Kasar Sin ta kan shigo da kayayyakin duwatsun karfe da iskar gas da ruwan inabi da wasu kayayyakin teku da dai makamantansu. Amma bayan barkewar cutar numfushi ta COVID-19 a shekarar 2020, gwamnatin Australiya ta bi sahun gwamnatin Amurka a fannonin siyasa da diflomasiyya, ta tayar da hankali tsakaninta da kasar Sin domin yunkurin hana ci gaban kasar Sin. Bisa wannan yanayin da ake ciki, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan mayar da martani, ta tsai da kudurin dakatar ko rage yawan kayayyaki iri 7, kamar lobster da alkama da sukari da ruwan inabi da katako da kwal da tagula, da take shigowa dasu daga kasar Australiya. Bugu da kari, a watan Nuwambar shekarar 2020 kawai, kasar Sin ta ki amincewa jiragen ruwa 82 masu dauke da kwal ton miliyan 8.8 da su tsaya a tasoshin ruwan kasar Sin, sannan gwamnatin kasar Sin ta shelanta buga karin haraji da kashi 212 cikin dari kan ruwan inabi da darajarsu ta kai dalar Australiya biliyan 1.2 da ’yan kasuwa suke shigowa dasu daga Australiya.

Ko da yake, kasar Sin ta rage shigo da kayayyaki daga kasar Australiya, amma yawan bukatun da ake da shi a kasuwar kasar Sin ba zai ragu ba. A ganina, kasashen Afirka za su iya fitar da kayayyakinsu zuwa kasar Sin domin biyan bukatun da Sinawa suke da shi. Alal misali, kasar Afirka ta kudu, ta kasance tamkar kasar Australiya, ita ma wata muhimmiyar kasa ce dake samar da ruwan inabi. A matsayin daya daga cikin kasashe 6 dake samar da inabi mafi yawa a duk fadin duniya, yawan ruwan inabi da kasar Afirka ta kudu ke samarwa ya kai kashi 3 cikin dari bisa jimillar yawan ruwan inabi da duk duniya ke samarwa, ita ce kuma kasa ta tara dake samar da ruwan inabi mafi yawa a duk duniya. A ’yan shekarun baya, yawan Sinawan da suke amincewa da ruwan inabi na kasar Afirka ta kudu ya karu cikin sauri. Sabo da haka, kasar Afirka ta kudu za ta iya yin amfani da wannan dama ta fitar da karin yawan ruwan inabi zuwa kasar Sin.

Cinikayyar amfanin gona tsakanin Sin da Afirka ta samu damar neman karin ci gaba_fororder_210425-sharhi-Sanusi-hoto2

Nahiyar Afirka tana dab da tekun Indiya da Atlantic, kuma tana da arzikin kayayyakin teku, kamar lobster da crab da dai makamantansu wadanda suke da inganci sosai. Galibin ’yan Afirka ba su da sha’awar cin kayayyakin teku, amma Sinawa sun shahara sosai wajen cin kayayyakin abinci iri iri, musamman kayayyakin teku. Sabo da haka, idan kamfanonin kasashen Afirka za su iya daidaita kayayyakin teku bisa ma’aunin tsabtace kayayyakin abinci na kasa da kasa kamar yadda ya kamata, tabbas ne za su sayar da su a kasuwar kasar Sin kamar yadda suke so. Bugu da kari, sauran kayayyakin da kasar Sin zata iya shigo dasu daga kasashen Afirka sun hada da Coco da Coffee da sauran amfanin gona, da duwatsun karfe da na tagulla da dai sauransu.

A ’yan shekarun baya, yawan amfanin gonar da ake shigo dasu kasar Sin daga Afirka yana karuwa da 17.3% a duk shekara, amma bai kai 4% bisa na jimillar kayayyakin amfanin gona da kasar Sin ke shigowa dasu daga duk fadin duniya ba. A bana, za a shirya taron ministoci na dandalin tattaunawa na FOCAC a kasar Senegal, inda bangarorin Sin da Afirka zasu tattauna abubuwan da zasu yi tare a cikin shekaru 3 masu zuwa. A ganina, kamfanonin bangarorin biyu za su iya yin amfani da wannan damar su shigo da karin kayayyakin amfanin gona daga Afirka domin biyan bukatun da ake da shi a kasuwar kasar Sin bayan an tsige kayayyakin bangaren Australiya.

Abokanmu ’yan Afirka, Sinawa na yin lale marhabin da samun kayayyakinku a kasuwannin kasar Sin! (Sanusi Chen)