logo

HAUSA

Wasu 'yan majalisar dokokin Amurka suna wasa da wuta lokacin da suke kalubalantar manufar kasar Sin daya tak a duniya

2021-04-24 15:52:24 cri

Wasu 'yan majalisar dokokin Amurka suna wasa da wuta lokacin da suke kalubalantar manufar kasar Sin daya tak a duniya_fororder_微信图片_20210424155039

Kwamitin Kula da Harkokin Waje na Majalisar Dattijan Amurka, ya zartar da "Dokar takara bisa manyan tsare-tsare ta 2021" a ranar 21 ga wata. Cikin daftarin dokar mai shafuna 200, akwai wurare sama da 50 da aka ambaci yankin Taiwan na kasar Sin, inda kuma aka bada shawarar cewa, ya kamata Amurka ta rika sayar da makamai a kai a kai ga Taiwan, da goyon bayan shigar Taiwan cikin kungiyoyin kasa da kasa, har ma da ba da shawarar cewa, ya kamata Amurka ta daidaita matsayin Taiwan ta yadda zai yi daidai da na gwamnatocin sauran kasashe.

Lallai Majalisar Dokokin Amurka na wasa da wuta a kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar kasar Sin! Wanda kuma takala ce kan manufar kasar Sin daya tak a duniya! Matakin da ya keta tanadin sanarwar hadin gwiwa guda uku dake tsakanin Sin da Amurka, da kuma keta alkawarin da Amurka ta yi wa kasar Sin kan batun Taiwan.

Kasar Sin daya ce tak a duniya. Wannan manufa kuma wata ka'ida ce da kasashen duniya suka amince da ita, kuma iyaka ce da Sin ta shata. Batun Taiwan, ba shi da muhallin sasanci a wajen gwamnatin kasar Sin.

Kasar Sin na gargadin Amurka da ta cika alkawuranta, kuma kada ta zama mai tufka da warwara, ta rika wasa mai hadari da batun Taiwan. Kasar Sin ta sha nanata cewa, a shirye take ta yi namijin kokarin ganin an cimma dinkewar kasar cikin lumana, amma a lokaci guda kuma, ba ta yi alkawarin kin yin amfani da sauran damarmakin da take da su ba, kana babu wani zabi da ta yi watsi da shi. Don haka, dangane da wannan batun, bai kamata wadansu Amurkawa su ci gaba da yaudarar kansu da kuma yanke hukunci na kuskure ba. (Bilkisu Xin)