logo

HAUSA

Akwai bukatar hadin kai na bangarori da dama wajen tinkarar sauyin yanayi

2021-04-23 20:47:27 cri

Akwai bukatar hadin kai na bangarori da dama wajen tinkarar sauyin yanayi_fororder_微信图片_20210423204604

A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin yanayi ta kafar bidiyo daga nan Beijing tare da gabatar da muhimmin jawabi. A cikin jawabin nasa, Xi ya ba da shawarar "kafa makomar bai daya ta bil’adama da halittu", kana ya gabatar da wasu ka'idoji da manufofi don cimma wannan buri. Musamman, ya yi kira ga kasashe daban daban da su martaba tsarin kasancewar bangarori daban-daban da daukar nauyi na bai daya bisa la’akari da bambancin dake akwai, wadanda suke a zahiri da fadakar da dan Adam ta yadda za a magance sauyin yanayi. Baya ga haka, Xi Jinping ya gabatar da jerin takamaiman matakai a yayin taron.

Mataimakin farfesa Anri Sharapov na kwalejin nazarin harkokin gabashin duniya na Tashkent dake kasar Uzbekistan na ganin cewa, a matsayinta na babbar kasa da ke sauke nauyi a wuyanta, kasar Sin ta nuna wa duniya aniyarta ta kare muhalli da magance matsalolin sauyin yanayi, wanda hakan zai karfafa gwiwar kasashen duniya wajen magance sauyin yanayi tare.

A lokaci guda, shugabannin yammacin duniya, ciki har da na Amurka da  Japan da Turai su ma sun sanar da burinsu na rage yawan gurbataccen hayaki da suke fitarwa. Irin wannan alkawarin da suka dauka yana da yakini, amma abu mafi mahimmanci shi ne cika alkawarin.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, ayyuka masu yawa da kasashen duniya suka gudanar wajen tinkarar sauyin yanayi ba su yi wani tasiri ba, babban dalili kuwa shi ne, wasu kasashen yamma ciki har da Amurka sun ki sauke nauyin dake bisa wuyansu.

Ban da wannan kuwa, bisa la'akari da bambance-bambancen dake kasancewa a matakan ci gaba, karfin tattalin arziki, da hanyoyin fasaha, bai dace ba kasashe masu tasowa su dauki nauyi daidai da na kasashe masu ci gaba. Musamman a yanayin da muke ciki na yakar cutar numfashi ta COVID-19, kasashe masu tasowa sun fi fuskantar karin matsaloli. Don haka, a matsayin ginshikin tafiyar da harkokin duniya, dole ne a kara karfafa manufar daukar nauyi amma bisa la’akari da bambancin dake akwai.

Game da haka, Xi Jinping ya yi kira ga kasashe masu ci gaba, da su kudiri niyya tare da daukar matakai, da samar da tallafi ga kasashe masu tasowa a fannonin kudi, da fasaha, da horo, da kaucewa kafa shingen cinikayya bisa dalili na kiyaye muhalli. Wannan shi ne bukatun da kasashe masu tasowa ke nunawa. (Bilkisu Xin)