logo

HAUSA

Xi ya halarci taron kolin shugabannin kasashen duniya kan sauyin yanayi

2021-04-23 14:00:32 CRI

Xi ya halarci taron kolin shugabannin kasashen duniya kan sauyin yanayi_fororder_210423-bayani-Maryam-hoto

Bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi masa, da daren jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin shugabannin kasashen duniya kan sauyin yanayi ta kafar bidiyo, inda kuma ya gabatar da muhimmin jawabi.

Cikin jawabinsa, Xi ya jaddada cewa, ya kamata mu nemi ci gaban kasa ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma goyon bayan hadin gwiwar dake tsakanin bangarori daban daban, da daukar alhakin dake wuyanmu yadda ya kamata, domin kafa makomar bai daya ta bil’adama da halittu.

Ga karin bayani daga Maryam Yang…

Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, gabanin matsalolin dake gabanmu ta fuskar kyautata muhallin kasa da kasa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara kuzari wajen hada kansu, domin fuskantar batun sauyin yanayi, da kuma neman hanyar samun daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. Yana mai cewa,“Sauyin yanayi na haddasa illa ga zaman rayuwar bil Adama, da bunkasuwar kasa da kasa, don haka ya kamata gamayyar kasa da kasa su dauki matakai don kafa makomar bai daya ta bil’adama da halittu. Matakin farko shi ne, mu nemi daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. Muhallin halittu na renon bil Adama, shi ya sa, ya kamata mu girmama muhalli, da bin muhalli, da kuma kiyaye shi.”

Mataki na biyu shi ne, mu nemi ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Kare muhallin halittu yana nufin kare karfin samar da kayayyaki, kuma kyautata mahallin halittu yana nufin raya karfin samar da kayayyaki. Ya kamata mu kawar da hanyoyin neman ci gaba masu gurbata muhalli, da kuma dukufa wajen yin kwaskwarima a fannnin tattalin arziki, da makamashi, da kuma tsarin masana’antu, ta yadda kyakyyawan muhalli zai kasance babban tushen samun dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya.

Mataki na uku shi ne, kyautata muhalli bisa tsarin da muka tsara. Muhallin halittu na kunshe da tsaunuka, da ruwa, da gandun daji, da gonaki, da rairayi da kuma ciyawa, ya kamata mu tsara shiri mai dacewa domin cimma burinmu na samun daidaituwar muhallin halittu.

Mataki na hudu shi ne, kare jama’a. Ya ce, bai kamata ba mu manta da aikin raya tattalin arziki da samar da guraben aikin yi, da kuma kawar da talauci, a yayin da muke neman hanyoyin kiyaye muhalli. Ya kamata mu aiwatar da aikin kare muhalli, tare da inganta yanayin adalci tsakanin kasa da kasa, domin kara tsaro da jin dadin zaman al’umma.

Mataki na biyar shi ne, tsayawa tsayin daka kan manufar hadin gwiwar tsakanin sassa daban daban. Ya kamata mu kare tsarin kasa da kasa bisa jagorancin MDD, da kuma bin manufofi da ka’idoji na “yarjejeniyar tsarin sauyin yanayi na MDD”, da “yarjejeniyar Paris”. Kasar Sin tana maraba da dawowar kasar Amurka cikin yunkurin daidaita sauyin yanayi na kasa da kasa, tana kuma fatan yin hadin gwiwa da kasar Amurka, da ma sauran kasashen duniya wajen karfafa ayyukan kyautata muhallin duniya.

Mataki na shida shi ne, daukar alhaki yadda ya kamata, ta hanyoyi mabambanta. Yana mai cewa,“Babban tushen tinkarar sauyin yanayi shi ne daukar alhaki cikin hadin gwiwa, amma ta hanyoyi mabambanta. Ya kamata mu girmama gudumamwar da kasashe masu tasowa suka bayar a fannin tinkarar sauyin yanayi, yayin da nuna tausaya musu kan matsalolin musamman da suke fuskanta. Ya kamata kasashe masu ci gaba su dauki matakai yadda ya kamata, domin ba da taimako ga kasashe masu tasowa, wajen gaggauta aikin neman bunkasuwa ta hanyoyin kare muhalli.”

Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta shigar da ra’ayin  kiyaye muhallin halittu da raya irin ra’ayin a cikin tsarin mulkin jamhuriyar jama'ar Sin, tare da shigar da su cikin tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin. Kana ta tsayawa kan hanyar ba da muhimmanci ga kiyaye muhallin halittu, da hanyar samun bunkasawa ba tare da gurbata muhalli ba. Ya ce,“Kasar Sin za ta himmantu wajen ganin ta kai ga matsayin koli game da fitar da hayaki mai dumama yanayi nan da shekarar 2030, zuwa samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060. Kuma, Sin ta yi alkawarin cewa, tsawon lokacin da kasar ta ke bukata wajen cimma wannan buri, ba zai kai na lokacin da kasashe masu ci gaba ke bukata ba, don haka, kasar Sin tana bukatar yin namijin kokari a wannan fannin.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)