logo

HAUSA

An rufe taron tattaunawa na Boao na kasashen Asiya na shekara-shekara na 2021

2021-04-22 14:26:18 CRI

An rufe taron tattaunawa na Boao na kasashen Asiya na shekara-shekara na 2021_fororder_src=http___mhw.1188fc.com_uploads_image_20190305_1551753256479813&refer=http___mhw.1188fc

Jiya Laraba ne aka rufe taron dandalin tattaunawa na Boao na kasashen Asiya na shekara-shekara na 2021, mai taken “Babban sauyin da duniya ke fuskanta: gudanar da harkokin duniya cikin hadin kai da aiwatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ tare”.

A gun taron manema labarai na rufe taron, babban sakataren dandalin tattaunawa na Boao, Li Baodong ya nuna cewa, bangarori daban-daban na jinjinawa gudunmawar da shawarar “ziri daya da hanya daya” ke bayarwa, wajen farfado da tattalin arzikin duniya, kuma sun yi kira da a kara hadin kai, don kiyaye tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban.

Ga cikakken bayanin da abokiyar aikinmu Amina Xu ta hada mana.

A gun taron manema labaran, babban sakataren dandalin tattaunawa na Boao, Li Baodong ya yi bayanin cewa, a matsayinsa na daya daga cikin wasu dandaloli mafi muhimmanci a duniya, dandalin Boao ya samu mahalarta da dama. Duk da ganin yadda cutar COVID-19 ke kan ganiyarta a duniya, an ce, mutanen da suka yi rajista ya haura 4000. Ban da wannan kuma, shugabanni da kusoshin kasashe 15, da manyan jami’an kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da ma manajoji fiye da dari na manyan kamfanoni dake kan matsayin koli 500 a duniya, har da masana da dama sun halarci wannan taro.

Li ya ce, shugabannin kasashe daban-daban da wakilan bangarorin siyasa da kasuwanci, sun ba da shawarwarinsu dangane da taken taro, ba ma kawai sun kai ga cimma matsaya daya game da bukatar hadin kan duniya wajen tinkarar cutar ba ne, har ma da batun kara karfin daidaita matsalolin duniya cikin hadin kai, tare da yin kira ga kiyaye manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da kara yin hadin kai da tuntubar juna. Ban da wannan kuma, an tattauna kan yadda za a yi hadin kai, don ganin an farfado da tattalin arzikin duniya, da samun bunkasuwa tare. Li ya ce:

“Cinikayya a tsakanin kasashe da shawarar ke shafa ta samu bunkasuwa, duk da yadda cutar ke ci gaba da addabar duniya. Saboda haka, wannan shawara ta zama abin dogaro wajen ba da tabbaci ga rayuwar al’umma. Ta wannan hanya za a iya yin sufurin kayayyakin kandagarki da samun kudade. Bangarori daban-daban na ganin cewa, wannan shawara ta zama mataki daya tilo, dake iya hada kanta da sauran manufofin raya kasa da kasa, da shawarwari tsakanin bangarori daban-daban.”

Bana ne ake cika shekaru 20 da kafuwar wannan dandali, saboda haka, ya kasance taron murnar cika shekaru 20 da kafuwarsa. Li ya ce, a cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, dandalin ya fuskanci sauye-sauyen duniya, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen cimma matsaya daya, tsakakanin kasashen Asiya da ciyar da bunkasuwar Asiya gaba daya, har ma da ba da gunduma wajen sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da bunkasuwa. Li ya ce:

“A cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, dandalin ya yi namijin kokari, wajen bayyana ra’ayi, da kuma shawarwari irin na Asiya, game da bunkasuwar nahiyar baki daya, bisa halin da kasashen nahiyar ke ciki. Dandalin bai taba mantawa da nauyin dake wuyansa, na dunkulewar bunkasuwar nahiyar da duniya baki daya ba. Kuma yana nacewa aniyyarsa ta bude kofa, da samun moriya, tare da kiyaye manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da goyon bayan MDD, ta yadda za ta taka rawarta mai muhimmanci.”

Ban da wannan kuma, Li ya yi nuni da cewa, idan an yi hangen nesa, dandali zai ci gaba da bayyana ra’ayin Asiya, da ma taka rawarsa, wajen ingiza bunkasuwar duniya baki daya. Abin lura shi ne, an yi taron tattaunawa tsakanin ’yan kasuwar Sin da Amurka a yayin taron Boao. Lokacin da ya yi tsokaci kan wannan batu, Li ya ce, an kwashe lokaci mai tsawo ana yin wannan taro, kuma a bana ya samu mahalarta wakilai da dama. Bangarorin biyu sun tattauna kan yadda za a warware takaddamar ciniki a tsakaninsu, da bullo da hanyoyin hadin kan bangarorin biyu a fannin ciniki da tattalin arziki, da bunkasa dangantaka irin wannan yadda ya kamata da sauransu. A cewarsa, ’yan kasuwannin bangarorin biyu sun cimma matsaya daya ta kara hadin kansu. Ya ce:

“A ganin ’yan kasuwannin kasashen biyu, ya kamata a kaucewa mai da dangantakar ciniki da tattalin arzikin su batun siyasa. Ba za a samu moriya idan kasashen biyu suka yanke hulda ba, wanda kuma hakan zai haifar da barazana ga tattalin arzikin bangarorin biyu, har ma duniya baki daya. Saboda haka, mahalarta taro na ganin cewa, kamata ya yi a kara yin sulhu bisa daidaito, don magance wadannan matsaloli cikin hadin kai.” (Amina Xu)