logo

HAUSA

Sin Ta Gabatarwa Duniya Shawarar Sin Na “Boao” Dangane Da Hadin Kan Kasa Da Kasa Da Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

2021-04-22 11:17:45 CRI

Sin Ta Gabatarwa Duniya Shawarar Sin Na “Boao” Dangane Da Hadin Kan Kasa Da Kasa Da Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20190504_ae2d9143e118449aace4f94150b9f8cf.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

“Yanzu muna cikin wani karni dake cike da kalubale da fata.”

An yi bikin bude taron dandalin tattaunawa na Boao na kasashen Asiya na shekara-shekara na bana a Boao dake lardin Hainan, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken “haye wahalhalu cikin hadin-gwiwa, kirkiro makoma da gina al’umma ta bai daya”.

Taken taro na wannan karo shi ne “Babban sauyin da duniya ke fuskanta: gudanar da harkokin duniya cikin hadin kai da aiwatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ tare”. Game da makomar Bil Adama, shugaba Xi ya ba da shawarwari guda hudu, wato yin shawarwari cikin daidaito da samun makomar da za ta amfani juna da cin moriya tare, da gaggauta yin kirkire-kirkire don raya makoma mai wadata da hadin kai don kyautata lafiyar Bil Adama da nacewa ga adalci da mutunta juna.

Na farko, tsayawa tsayin daka kan ka’idar yin shawarwari da cin moriya tare da nacewa ga manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da kiyaye tsarin duniya karkashin jagorancin MDD, da kiyaye dokokin kasa da kasa da tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban bisa tushen WTO, ta yadda za a ingiza tsarin daidaita harkokin duniya.

Na biyu, nacewa ga tunanin bude kofa da yin kirkire-kirkire. Kamata ya yi an ingiza ciniki da zuba jari cikin ‘yanci da zurfafa dunkulewar tattalin arzikin shiyya-shiyya da inganta tsare-tsaren samar da kayayyaki. Ban da wannan kuma, gaggauta dangantar hadin kai mai nasaba da cinikayya ta yanar gizo. Amfani da dama mai kyau na kwaskwarimar da aka yiwa fannin kimiya da fasaha da sana’o’i daban-daban ta yadda al’ummar duniya za su ci gajiya.

Na uku, kamata ya yi kasashen duniya su kara hada kai saboda ganin bayan cutar COVID-19 ke ci gaba da addabar sassan duniya, ta yadda za a haye wahalhalu tare. Ban da wannan kuma, kamata ya yi kasashen duniya su kara hadin kansu a fannin kandagarki da rarraba rigakafi. Dadin dadawa, dole ne kasashen duniya su yi namijin kokari yin hadin kai don tinkarar matsalar kiwon lafiya da sauyin yanayi da sauran kalubaloli tare.

Na karshe kuma, ingiza hadin kan kasashen duniya wajen tafiyar da harkokin duniya da kyautata karfi da tsari masu nasaba da hakan. A sa’i daya kuma, yin watsi da tunani na wani bangare daya dake samun riba, ta yadda tilas sai wani bangare na daban ya yi hasara, don kafa sabon nau’in dangantakar duniya da raya makomar Bil Adama ta bai daya. Bai kamata bunkasuwar wata kasa ta zama dalilin da ya sa sauran kasashe su matsa mata lamba ba, kamata ya yi kasashen duniya su nace ga adalci da mutunta juna da zaman lafiya da bunkasuwa da daidaito da bin tsarin demokuradiyya da ‘yancin kai, wadanda suke zama burin bai daya na Bil Adama.

Sin tana iyakacin kokarinta na samarwa duniya gudunmawa wajen samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, a wannan karo kuma, ta hanyar wannan dandali tana kokarin hada karfi da basirar ragowar kasa da kasa don gabatar da shawarar taron dandalin “Boao” ga duniya. (Amina Xu)