logo

HAUSA

Kwallon kwando ya haskaka rayuwar masu ritaya

2021-04-22 15:16:55 CRI

Kwallon kwando ya haskaka rayuwar masu ritaya_fororder_0422-1

Sau da dama akan yi tambayar cewa, me mutum ya fi dacewa ya yi bayan kammala aiki, wato bayan ya yi ritaya ko kuma shekarun sa sun kai 60 a duniya? Kula da jikoki, ko dai kawai zama a gida? A birnin Changsha dake lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, wasu mata da suka yi ritaya sun zabi haskaka rayuwar su ta hanyar yin wasan kwallon kwando.

Wadannan mata sun sanyawa kungiyar su suna Feiyue, wadda ke kunshe da mata masu matsakaitan shekarun haihuwa 60.

Daya daga ‘yan wasannan kulaf mai suna Li Ying, ta yi wasa da kwallo, ta keta bangaren tsaron baya, ta juya ta kuma jefa kwallo a raga. Kwallon ta shiga zare tare da sauka kasa yadda ya kamar.

Shekaru 10 da suka gabata, bisa sha’awar su ta buga kwallon kwando, wadannan mata suka kafa wannan kungiya. Shugabar su Xiao Jing ta ce "Rayuwa bata takaita kan kwallon kwando kadai ba, amma kuma ba za ta yiwu, ba tare da kwallon ba."

Xiao Jing da Li Ying, sun shafe shekaru sama da 40 suna buga wannan wasa. Sun koyi wasan tare, tun suna kanana a makarantar koyar da wasanni. Duk kuma da cewa ba su buga wasan a matsayi na ajin kwararru ba, sun ci gaba da yin sa har suka kammala makaranta, kuma da yawa daga abokan aikin su, na kallon su a matsayin kwararru a fannin wasan kwallon kwando.

Da take tsokaci game da hakan, Li ta ce "Ko da na jima ban buga wasan ba, idan na dauki kwallo, na kan ji kamar tana likewa a hannu na. ba mai iya karbe ta daga gare ni,".

Da yawa daga mambobin kungiyar sun taba yin wasanni a baya. Wasu sun taba yin iyo, ko tsere a lokacin da suke makaranta. Ko shakka ba bu, kungiyar na cike da kuzari irin na al’ummun Asiya a tare da ita.

A lokaci guda kuma, sun zamewa kan su masu horaswa. Daya daga cikin su ta duba yanar gizo ne, inda ta karanta bayanai game da abokan wasan ta, nan da nan kuma ta nuna bukatar shiga kungiyar, ba tare da ta san wani abu game da kwallon kwando ba. Manyan cikin kungiyar ne ke bayyana ka’idojin yadda za a tafiyar da wasan a kan su, su suke nuna dabarun wasan, kafin a jima su ma sabbin zuwa sun zama kwararru.

Xiao ta ce "Wasu mutanen kan ce, ta yaya mata masu shekaru 60 za su iya yin wasan kwallon kwando? Amma a kalle mu, muna jin kamar mu yi ta kewaya wannan fili!"

Dabi’ar yin wasan kwallon kwando akai akai, ta sanyawa wadannan dattijai mata karsashi. A yanzu suna iya yin wasa cikin sauri da karfin jiki. "A tsawon shekaru, ba kasafai muke rashin lafiya ko kwanciya a asibiti ba," a cewar Xiao.

Baya ga karfin jiki na zahiri, wata karin riba da matan ke samu daga kwallon kwando ita ce zuciya mai tashen lafiya, da kuma nutsuwar rai. Xiao ta ce "Muna yin atisaye sau biyu a duk mako, kuma ba ma jin gajiya, ko da mun ci gaba da buga wasa har tsawon sa’a guda. A duk lokacin da muke da lokaci, za mu iya buga wasa na tsawon lokaci"

Cikin shekaru 10 da suka gabata, dukkanin ‘yan wannan kungiya suna yin gumi, suna gudu da jin dadin nasarorin su tare. Ana iya jin dariyar su da Shewa cikin filin wasa.

Li ta ce "shawarar wasan, da kaunar da muke yi masa ce ta hada mu wuri guda. Ko shakka ba bu, shekaru lambobi ne kawai a gare mu, amma ba su takaita mu ba". Xiao ta kara da cewa, mata masu shekaru irin na su, baya ga kula da harkokin gida, suna kuma iya samarwa kan su abubuwan nishadi don karawa rayuwa moriya ta hanyar wasanni.

Bayan busa usir na karshen wasa a duk rana, sai ‘yan wasan su taru domin sanya rana ta gaba ta sake haduwa domin buga kwallo.

A duk lokacin da Li Ying ke buga wasa tare da dattijuwa abokiyar wasanta, wadda a bana take cikia shekaru 65 da haihuwa, ta kan yi tunanin kasancewa irin ta a nan gaba. Takan ce a ran ta "Muddin za a iya buga wasa, to a ci gaba da bugawa kawai."