logo

HAUSA

Magudin siyasa da Australiya ta yi abin dariya ne

2021-04-22 20:58:11 cri

Magudin siyasa da Australiya ta yi abin dariya ne_fororder_微信图片_20210422205734

Jiya Laraba ne, ministan harkokin wajen Australiya ya sanar da yaga takardar bayani da kuma tsarin yarjejeniya game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da aka kulla tsakanin Sin da gwamnatin jihar Victoria ta kasar bisa hujjar cewa, "ba su dace da manufar diplomasiyya ta Australia ba ko kuma ba za su amfana wa dangantakar diflomasiyya a tsakaninmu da sauran kasashe ba. " Wannan wani yunkuri ne da wasu 'yan siyasar Australiya dake da nufin kara tozarta kasar Sin don faranta ran "babbar yar'uwa" Amurka domin su samu moriya a fannin siyasa.

Yayin da ake tuntubar cewa Majalisar Dokokin Amurka tana inganta "Dokar takara bisa manyan tsare-tsare ta 2021" tare da bukatar gwamnatin Biden da ta aiwatar da cikakkiyar manufar "takara bisa manyan tsare-tsare" tare da kasar Sin, wannan mummunan magudin siyasar da kasar Australiya ta yi ba abin mamaki ba ne.

Idan aka yi la’akari da matsayin Australiya a duniya, matakin da gwamnatin kasar ta dauka, ba zai yi wani babban tasiri kan aikin raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” ba. Sabanin haka, hakan zai bai wa duniya damar kara ganin mummunar dabi’ar ‘yan siyasar Australiya da Morrison yake wakilta, da kuma bambancin dake tsakanin kalamansu da abin da suke aikatawa.

A cikin shekaru fiye da bakwai da suka wuce, nuna shakku da bata suna da ake yi kan shawarar "Ziri daya da hanya daya", ba su taba yin wani tasiri ga sha’awar yawancin kasashe na shiga shawarar ba. Ya zuwa watan Nuwamba na shekarar 2020, kasar Sin ta rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa guda 201 don raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” tare da kasashe 138 da kungiyoyin kasa da kasa 31. Magudin siyasa da wasu 'yan siyasan Australiya suka yi, ba zai iya hana ci gaban shawarar “Ziri daya da hanya daya” ba, sai ma ya zubar da martaba da kimar kasar Australiya ne kawai, sannan za’a rika yi mata dariya a fagen siyasar duniya. (Bilkisu Xin)