logo

HAUSA

An shirya gasar Shougang ta maraba da karatowar gasar Olympics ta birnin Beijing ta lokacin hunturu

2021-04-22 14:34:20 CRI

An shirya gasar Shougang ta maraba da karatowar gasar Olympics ta birnin Beijing ta lokacin hunturu

A ranar 11 ga watan Afirilun nan ne, aka gudanar da wata gasa mai lakabin “Shougang”, a lambun shakatawa na Shougang dake birnin Beijing. Wani sabon nau’in wasa ne da aka kirkira a bana, wanda ya samu mahalarta mutane 500 daga sassan rayuwa daban daban.

Da misalin karfe 10 na safiyar ranar, daukacin masu shiga gasar sun dau hanya, daga babbar kofar lambun ta kudanci. Kuma bisa ka’idar gasar, an raba masu shiga zuwa rukunoni daban daban, kuma a duk rukuni mutanen ciki na rike da na’urar auna kusurwa da kuma taswira, kana za su yi gudu da tafiya zuwa wurare 20, da suka hada da yankin tafkin Xiu, da hanyar sama, da koramar Qunming bi da bi.

‘Yan wasan za su ziyarci wurare muhimmai, kamar wurin wasan tsalle a kankara na dandalin “Beijing Winter Olympics” da hanyar iska ta dandalin ba da horo, na cibiyar wasannin kankara na birnin Beijing. Kyaftin din babbar kungiyar kwallon kwando kasar Sin ajin maza, wanda kuma ya halarci wannan gasa, ya bayyana cewa, "A yau, mutane da dama dake sha’awar wasanni sun shiga wannan wasa. Ya ce yana matukar farin ciki da ganin yadda kowa da kowa ke shiga harkokin wasannin motsa jiki. Ya ce “A matsayina na dan wasa, zan taka rawar gani wajen jagorantar wannan lamari, ina fatan karin mutane za su samu dama ta shiga wuraren wasanni daban daban don su nishadantu”. Ya ce wannan muhimmin mataki ne, na ba mu damar nuna kwarewar mu ta raya wasanni."

A matsayin dabarar samar da sauyi da raya wasanni rukunin Shougang, da hukumar wasanni ta Shougang, da kungiyar wasan kwallon kwando ta Beijing Shougang dake matsayin jigo, na ci gaba da lalubo hanyoyin da za su baiwa al’umma damar shiga a dama da su, a wasanni da ake shirya gasannin su, a lokaci guda kuma, hakan na hade wasannin da ake shirya gasar su a matakin kasa, da dabarar kirkirar sabbin dabarun raya wasanni ko ​​"Sports +" a turance. Hakan ya sa aka samar da wannan gasa da aka kirkira, aka kuma gabatar da ita a lambun shakatawa na Shougang. Wannan dabara ce ta sanya karin mutane da dama samun kafar shiga a dama da su, a gasanni, da cin gajiya daga wasannin.

Liang Zongping, mamba ne a kwamitin dindindin na kwamitin kolin JKS mai lura da gasar Shougang, shi ne kuma darakta, kuma shugaban kungiyar ‘yan kwadago, sakataren jam’iyya mai aikin lura da gasar Shougang, ya bayyana cewa, wannan gasa da aka gudanar a birnin Beijing, wato Shougang, tana da fifiko na kwararru, za ta kuma fadada damar shiga wasanni kala kala a fannoni da dama".

Liang Zongping ya ce "A wannan gasa, dabarar kirkirar wasanni ta ba da damar inganta karin wasanni da za a shigar cikin gasar lambun shakatawa na Shougang, tare da karfafa ci gaban lambun a nan gaba, ta hanyar shigar da manufar kasa ta raya wasanni, da kara wasanni, da shigar da kayatattun al’adun kasa cikin gasannin.

Wasan tsere da gano hanya, daya ne daga wasannin gasar Shougang, baya ga wasan kwallon kwando, da hockey na kankara, da baseball, da kwallon tebur. Muhimmin burin dai shi ne, samar da sabon salo na tsara wasanni. A nan gaba, wasannin Shougang za su kuma samar da wata dama, da kirkirar wasan tsare, da gano hanya da ake yi a cikin lambun shakatawa, da wanda ake yi tsakanin kasashe, wanda dukkanin su za su zamo wata kafa, ta yayata raya yawon shakatawa. A lokaci guda kuma, a bana ake cika shekaru 100 da kafuwar JKS, lokacin da kuma aka fara lasafta wa’adin da ya rage, kafin zuwan gasar hunturu ta Olympics, wadda birnin Beijing zai karbi bakunci.

Liang Zongping ya ce, “Muna nazari game da yiwuwar shirya wata gasa mai take na daban, nai nasaba da gasar hunturu ta birnin Beijing dake tafe. Fatan dai a cewar sa shi ne, kara fadada aiwatar da manufar kasar Sin, ta kirkiro hanyoyin bunkasa wasanni, ta yadda hakan zai dace da burin kasar na raya motsa jiki, tare da fadada kuzarin al’umma wajen rungumar wasanni, tare da tabbatar da cewa, Sinawa na kallon hakan a matsayin nauyin dake wuyansu na kyautata zamantakewa.