logo

HAUSA

Xi Jinping: Bunkasa ilimin kimiyya hanya ce ta ingiza ci gaban kasa

2021-04-22 16:25:03 CRI

Xi Jinping: Bunkasa ilimin kimiyya hanya ce ta ingiza ci gaban kasa_fororder_微信图片_20210422162254

Yayin da jami’ar Tsinghua ta kasar Sin ke cika shekaru 110 da kafuwa, shugabannin kasar Sin na kara jaddada muhimmancin inganta sha’anin koyo da koyarwa, a matsayin wani jigo da zai ingiza sassan ci gaban kasar Sin mai halayyar musamman ta gurguzu, wadda ke da burin farfado da dukkanin al’ummunta, da bunkasa ci gaba mai dorewa.

A yayin da ya ziyarci jami’ar ta Tsinghua a baya bayan, gabanin bikin cikar ta shekaru 110 da kafuwa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda shi ma tsohon dalibin jami’ar ne, ta jaddada bukatar samar da jami’o’i mafiya inganci, wadanda za su dace da yanayin musamman na kasar Sin, irin wadanda za su wuce gaba wajen ba da cikakkiyar gudummawa ga raya kasa da kyakkyawar zamantakewar daukacin al’ummar Sinawa.

Ko shakka babu, kalaman shugaba Xi na karfafa gwiwar jami’ar Tsinghua a fannonin bunkasa kirkire-kirkire da kere-kere, da renon dalibai da za su zamo masu hazakar ingiza ci gaban kasa bisa jigon kimiyya, sun dace da ra’ayoyin masana, sun kuma yi daidai da irin nasarori da kasar Sin ta cimma a zahiri, cikin shekarun da ba su wuce rabin karbi ba, tun bayan fara aiwatar da manufofin gyare gyare a gida da bude kofa ga waje.

Ko shakka babu, ziyarar shugaban Sin wannan jami’a ta jaddada manufar gwamnatin Sin, don gane da dora muhimmancin kan raya ilimi, musamman ma sassan binciken kimiyya da fasaha, da kirkire kirkire a fannonin.

Kamar dai yadda bahaushe kan ce “Ilimi gishirin rayuwar duniya”. Ga  duk mai bibiyar irin ci gaba da kasar Sin ta samu, ba zai manta da nasarorinta a fannin yaki da talauci, da shawo kan annobar COVID-19, da karin kumbuna, da taurin bil adama da ta cimma nasarar harbawa sassan duniyoyin dake wajen duniyar bil adama ba. Dukkanin wadannan nasarori ne masu nasaba da irin gajiyar da Sin ke ci daga ilimin kimiyya da fasaha, da sauran ilimomi masu alaka da hakan.

Ko da fannin raya ci gaban tattalin arziki da kasar ta samu tagomashin sa a shekarar bana, yayin da kasashe da dama ke fafutukar fita daga matsin da annobar COVID-19 ta jefa su, yana nuna yadda mahukuntan kasar Sin ke bin salon amfani da dabarun zamanintar da ci gaba, karkashin manufofin raya ilimi.

Ana ma iya cewa, sauran sassan duniya na da damar koyi da kasar Sin, a fannin raya ilimi, musamman ma fannonin kimiyya dake zama wani jigon cin gajiyar rayuwar bil adama a wannan zamani, da ma sauran zamunna dake tafe. (Saminu Hassan)