logo

HAUSA

Wane Ne Ya Daurewa ’Yan Sanda Amurka Gindi Har Suke Dukan Sojojin Kasar?

2021-04-21 13:48:06 CRI

Wane Ne Ya Daurewa ’Yan Sanda Amurka Gindi Har Suke Dukan Sojojin Kasar?_fororder_359b033b5bb5c9eaada534579d3ee3083af3b33b

A kwanakin baya ne George Floyd wani bakar fata ya gamu da ajalinsu sakamakon yadda wani dan sandan Amurka farar fata ya danne wuyansa da kafarsa har na tsawon mintoci 7 ba tare da ya nuna wata adawa ba, abin da ya girgiza kasashen duniya sosai. Amma, wasu sun ce Floyd ya yi amfani da takardar kudi na jabu, ya kuma taba yin ta’ammali da miyagun gwayoyi, sanna ya taba aikata laifufuka, a ganinsu sun fahimci matakin da ’yan sanda suka dauka, ba shi da alaka da matsalar bambancin launin fata. To, bari mu duba wannan lamarin da ya jawo hankali mutane sosai a shafin yanar gizo.

Caron Nazario wani bakar fata ne mai mukamin laftana a sojin Amurka sanye da inifom din soja, ya sayi wata sabuwar mota a kan hanyarsa ta komawa gida da kuma lasisinsa na wucin gadi, inda ya gamu da dan sanda Daniel Crocker da abokin aikinsa, sai suka bukaci Nazario da ya tsaya. Nazario ya nemi wani wuri dake da haske ya tsaya, amma wadannan ’yan sanda sun nunawa Nazario bindiga, inda suka ba shi izni da ya karya doka, alal misali sun bukaci Nazario da ya bude kofar motarsa, wani lokaci kuma sun neme shi da ya kau da hannusa daga kofar mota. Har sun fesa masa wani ruwa mai sa kwalla a fuskarsa. Ganin haka Nazario ya tambaye su cewa, ni da nake kokarin bautawa kasarmu don me kuka yi min haka? Amma, wadannan ’yan sanda biyu sun duka shi sun kuma sanya masa ankwa a hannu. A karshe, bayan da suka tabbatar da cewa, Nazario ba shi da wata matsala, sai suka gargade shi da kada ya yi kararsu, idan kuma ya yi, to za su mai da martani kansa.

Haka kuma wasu ’yan sanda a kasar ta Amurka, sun duka wani soja dake sanye da inifom, yana tuka sabuwar motarsa akan hanyarsa ta komawa gida, ba tare da wani dalili ba, inda suka yi masa barzana, don me ba a girmama sojan Amurka, ko kuma don me ’yan sanda suka duka sojin kasar ba tare da wani dalili ba?

To, bari mu ga wasu abubuwa masu muhimmanci game da wannan batu, sojoji bakaken fata, lasisin wucin gadi, sanya Inifom. Idan wannan soja ba bakar fata ba, ko za a duka shi? Idan Nazario ba ya sanye da inifom din soja ko shi ma abin da ya faru da George Floyd ka kya samun sa? Idan Nazario bai tsaya a wuri mai haske ba, da za a samu aukuwar irin wannan mummunan lamari?

Lokacin da Nazario ya shiga wannan hali , ya ce, me ya faru? Ina jin tsoro. Sai ’yan sandan sun amsa masa cewa, dole ne ka ji tsoro, dole ne a yanke maka hukuncin kisa.

Nazario ba farar hula ba ne, shi wani soja ne, don haka ya kai kara a gaban kotu tare da gabatar da shaidu da yake da su, inda ya zarge ’yan sanda da yin amfani da karfin tuwo, da nuna bambancin launin fata.

Idan har ana nuna shakku kan shaidu game da kisan Floyd, to yaya batun Nazario? A matsayinsa na soji mai bautawa kasar, amma an nuna masa karfin tuwo, har ma da yi masa barazana, saboda shi bakar fata ne kawai. Don haka, mun iya ganin cewa, bakaken fata a Amurka suna cikin mawuyacin hali. Yanayin kare hakkin Bil Adama na kara tsananta a Amurka, amma gwano ba ya jin warin jikinsa, Amurka ta kan tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe, ta hanyar fakewa da batun hakkin Bil Adama, alal misali ta shafawa kasar Sin bakin fenti da yayata jita jita kan wasu batutuwa ciki hadda yankin Xinjiang, da nufin dakile da kawo baraka a kasar Sin don hana bunkasuwarta. Wannan na nuna cewa, ’yan siyasar Amurka ba sa kula da batun hakkin Bil Adama ko kadan, suna mai da hankali kan muradunsu na siyasa ne kawai. (Amina Xu)