Ana samun ci gaba a tattaunawar nukiliyar Iran
2021-04-21 10:19:39 CRI
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce ana samun ci gaba a sabon zagayen tattaunawar da ake yi a Vienna, dangane da batun nukiliyar kasarsa, duk da kalubalen da ake fuskanta.
An ci gaba da tattaunawar diflomasiyya jiya a Vienna, domin farfado da yarjejeniyar kasa da kasa ta nukiliyar Iran da aka rattabawa hannu a shekarar 2015, inda dage takunkuman da aka sanyawa Iran din da batun nukiliyarta suka kasance a kan gaba cikin ajandar tattaunawar.
Gidan talabijin na Press na kasar Iran, ya ruwaito cewa, bayan tattaunawa da sauran wakilan kasashen dake cikin yarjejeniyar da suka hada da Birtaniya da Sin da Faransa da Rasha da Jamus, Abbas Araqci, ya ce Tehran za ta dakatar da tattaunawar a duk lokacin da tattaunawar ta kai ga tsananta sharudda ko bukatu ko aka fara bata lokaci.
Mataimakin sakatare janar kuma daraktan harkokin siyasa na sashen kula da harkokin wajen EU, Enrique Mora, wanda shi ne ya jagoranci tattaunawar ta jiya Talata, ya ce an samu ci gaba cikin makonni biyun da suka wuce, amma ana bukatar aiki tukuru. Kana an kafa wani rukunin kwararru na 3, wanda zai magance batutuwan da za su biyo baya. (Fa’iza Mustapha)