logo

HAUSA

Don me kasar Sin ta gabatarwa duniya shawarar “ziri daya da hanya daya”?

2021-04-21 20:03:14 CRI

Don me kasar Sin ta gabatarwa duniya shawarar “ziri daya da hanya daya”?_fororder_1

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi ta kafar bidiyo a yayin bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Boao jiya Talata, inda ya nanata cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” wata babbar hanya ce mai makoma mai haske da kowace kasa za ta iya shiga a dama da ita, ba karamar hanya mallakin wata kasa daya kacal ba ne. Wannan furucin nasa ya bayyana ainihin ma’anar shawarar.

Shin me ya sa kasar Sin ta gabatarwa duniya wannan babbar hanya mai haske? Amsar ita ce, saboda za ta iya taimakawa kasashen duniya tinkarar kalubalen da suke fuskanta, da samar da karfin kirkiro kyakkyawar makoma.

Muna iya ganin yadda shawarar “ziri daya da hanya daya” ta taimaka sosai ga ayyukan yaki da cutar mashako ta COVID-19, kana tana taimakawa kasa da kasa farfado da tattalin arzikinsu.

A wannan karo, kasar Sin ta bada shawarar kara inganta dangantakar abokantaka, da raya harkokin kasuwanci ta yanar gizo bisa hanyar siliki, ta yadda za’a saukakawa kasashen da abun ya shafa matakan zuba jari da hadin-gwiwa.

Don me kasar Sin ta gabatarwa duniya shawarar “ziri daya da hanya daya”?_fororder_2

Abun lura a nan shi ne, tun farkon gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, tana maida hankali kan raya makoma mai haske ga bil’adama, musamman raya harkoki ba tare da gurbata muhalli ba, ciki har da inganta ababen more rayuwar al’umma, da bunkasa makamashi mai tsabta, da kyautata kawancen samar da ci gaban kasa da kasa da sauransu ba tare da gurbata muhalli ba.

Bugu da kari, rahoton bankin duniya ya nuna cewa, zuwa shekara ta 2030, ana sa ran raya shawarar “ziri daya da hanya daya” zai taimakawa mutane miliyan 7.6 fita daga matsanancin talauci, kana wasu kimanin miliyan 32 za su fita daga matsakaicin talauci. Wato idan shawarar “ziri daya da hanya daya” ta zama hanyar rage talauci har ma da samar da ci gaba, duniya za ta kara zama mai bude kofa da hakuri.

A halin yanzu, shawarar “ziri daya da hanya daya” tana samun karbuwa sosai a fadin duniya baki daya, al’amarin da ya tabbatar da cewa, nuna adalci da neman samun moriyar juna cikin hadin-gwiwa, ita ce hanya madaidaiciya. Kamar yadda shugaba Xi ya fada a jawabinsa, “muna cikin zamanin dake cike da kalubaloli, amma kuma yana cike da damammaki.” (Murtala Zhang)