logo

HAUSA

Wang Qishan ya halarci taron shekara shekara na dandalin BFA na bana

2021-04-21 12:45:33 CRI

Jiya ranar 20 ga wata, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan, ya halarci bikin bude taron shekara shekara na dandalin tattaunawar kasashen Asiya na Boao wato BFA, da ake yi a birnin Boao da ke lardin Hainan na kasar Sin, inda ya gana da membobin hukumar kula da ayyukan dandalin, da ma wasu abokan hadin kai, kana da ya yi shawarwari tare da wakilan kamfanonin Sin da na waje.

A yayin bikin bude taron, Wang Qishan ya bayyana cewa, Shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta bidiyo a gun bikin, inda ya bayyana matsayin kasar Sin, da ma dabarunta kan yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar Asiya da ma duk duniya, gami da nuna goyon bayan ci gaban dandalin da gwamnatin Sin ke yi.

Ban da wannan kuma, Wang ya ce, babban taken taron shi ne “Sauyin duniya: Tattaunawa kan ayyukan tafiyar da harkokin duniya, da ma kokarin samun bunkasuwa bisa shawarar ‘ziri daya da hanya daya’”, inda aka nuna matsalolin dake gaban duniya, wadanda ke bukatar a warware su cikin gaggawa, tare da burikan da kasashen duniya ke son cimmawa.

A cikin jawabin Xi, ya bayyana matsayin kasar Sin har sau biyu, wato a hada kai maimakon jawo baraka, a hada gwiwa maimakon adawa da juna, kana a bude kofa maimakon rufe ta, a martaba ra’ayin cudanyar bangarori da dama, da ma yada ra’ayin tunanin darajta bil Adama. Ya ce ya kamata a gaggauta raya makomar bil Adama ta bai daya, ta hanyar samun bunkasuwa bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”. (Kande Gao)