logo

HAUSA

An mai da hankali kan ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kawar da talauci a dandalin Boao

2021-04-21 14:04:27 CRI

An mai da hankali kan ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kawar da talauci a dandalin Boao_fororder_0421-bayani-Bello

A ranar 19 ga wata, an shirya taron tattauna batun rage talauci, da samun ci gaban kauyuka mai dorewa, a gefen dandalin tattaunawar hadin kan kasashen Asiya na Boao, wanda ke gudana a garin Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.

Kasar Sin ta sanar da kawar da talauci a dukkan yankunanta a farkon bana, batun da ya nuna cewa, an samu fitar da mutane miliyan 98.99 dake zama a cikin kauyuka daga kangin talauci, da daidaita matsalar talauci a wasu gundumomi 832, da kauyuka dubu 128. Dangane da lamarin, darektan hukumar raya kauyuka ta kasar Sin Wang Zhengpu, ya bayyana a wajen taron tattaunawar da ya gudana a ranar 19 ga wata cewa,

“Yadda aka cimma nasarar kawar da talauci a kasar Sin, ya baiwa dimbin mutanen kasar damar kyautata zaman rayuwarsu, da cimma burikan da suka sanya gaba, da zamanintar da wuraren da suka taba fama da matsalar talauci a baya, da samar da manyan sauye-sauye a wurare daban daban na kasar. Ta wannan hanya, kasar Sin ta samu ci gaba sosai, a kokarinta na kafa yanayin zaman al’umma mai walwala, da yunkurin neman cimma burinta na samun ci gaban kasa. Haka zalika, kasar Sin ta samar da gudunmawa ga aikin kawar da talauci a duniya, musamman ma a fannin raba fasahohin da ta samu ta hanyar gudanar da gwaje-gwaje a gidanta.”

Wani misali game da yadda kasar Sin ta samu nasarori a kokarin raya kasa da rage talauci, shi ne yadda lardin Hainan, da ake gudanar da dandalin Boao a duk shekara, ya samu raya kansa, daga wani tsibirin dake fama da koma bayan tattalin arziki, zuwa wani yanki mai ci gaba da ke iya karbar bakuncin manyan bukukuwan kasa da kasa. A cewar Li Jun, mataimakin sakataren reshen ofishin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a lardin Hainan, babban ci gaban da aka samu a lardin Hainan a fannin rage talauci wani abu ne da kowa ya gani, ya ce,

“Yadda ake samun ci gaba sosai a Hainan wani misali ne na babban ci gaban da aka samu a wurare daban daban na kasar Sin. A lardinmu kadai, mun samu fitar da mutane dubu 649 da dari 7 daga kangin talauci.”

A cewar Li, yanzu haka wata waka ta zama mai farin jini sosai tsakanin mutanen da suke zama a yankunan kauyukan lardin Hainan, wadanda suka taba fama da talauci a baya. Wani bangaren wakar na cewa:

“Babu sake damuwa game da batun neman gidan da zai iya kare mutum daga iska da ruwa. Babu damuwar ganin likita. Mun riga mun kawar da talauci, ga gidajen zama masu kyan gani. Gaskiya ina jin dadin zaman rayuwa, ko a cikin mafarki ma ina ta murmushi.”

A nashi bangare, mataimakin ministan raya tattalin arziki na kasar Italiya, kana wani shehun malami mai nazarin ilimin hada-hadar kudi, Michele Geraci, wanda shi ma ya halarci taron tattaunawar batun rage talauci da raya kauyuka, ya nuna yabo kan ci gaban da kasar Sin ta samu, a kokarin rage talauci. Ya ce, dabarar da kasar Sin ta dauka ta “tallafawa marasa karfi bisa bukatunsu” fasaha ce mai kyau. Ya kamata dukkan kasashen da suke fuskantar matsalar talauci su yi koyi da wannan dabara ta kasar Sin. Mista Geraci ya ce,

“Kasar Sin ta gabatar da manufar ‘tallafawa mutane marasa karfi bisa bukatunsu’, da kafa wani tsarin da ya kunshi dukkan bayanai game da mutanen da suke fama da matsalar talauci, ciki har da sunayensu, da bayanan iyalansu, da dai sauransu. Hakika ana samun matsalar talauci a wurare daban daban. Ba a nahiyoyin Afirka da Asiya kadai ake samunta ba, har ma ana da ita a manyan birane irinsu London da Rome. Wato matsalar ta kasance wani kalubalen da kasashe masu tasowa da masu sukuni dukkansu suke fuskantar. Don haka, ya dace dukkanmu mu yi kokarin koyon fasahohi masu kyau da kasar Sin ta samu, musamman ma dabararta ta tallafawa mutane marasa karfi bisa bukatunsu.”

A cewar darektan hukumar raya kauyuka ta kasar Sin, Wang Zhengpu, kasarsa na son yin amfani da dandalin tattaunawa na Boao, da sauran bukukuwan kasa da kasa, don karfafa hadin gwiwarta da sauran kasashe ta fuskar aikin rage talauci, tare da samar da gudummawa ga yunkurin kawar da talauci baki daya daga doron kasa. (Bello Wang)

Bello