Taron dandalin Boao na shekarar 2021
2021-04-21 09:38:22 CRI
A wannan makon ne, aka bude taron dandalin tattaunawa na Asiya na Boao da aka saba gudanarwa a kowace shekara, a Bo’ao, wani karamin gari dake lardin Hainan a kudancin kasar Sin, wanda ya yi suna saboda shirya taron shekara-shekara na dandalin wanda a wannan karo kimanin halartar baki sama da 2600 daga kasashe da yankuna fiye da 60 suka halarta.
An kafa dandalin ne a shekarar 2001, da zummar kara dunkulewar tattalin arzikin shiyyar tare da kara kusanto da kasashen nahiyar Asiya domin cimma muradunsu na ci gaba.
Dandalin na Boao zai kuma taimakawa kasashen Asiya da duniya baki daya, wajen cimma matsaya kan yadda za a samar da bunkasuwa da suke fasalta imanin da ake da shi game da ci gaba, bayan yaki da annobar COVID-19.
Ana kuma fatan dandalin zai mayar da hankali kan hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da hade shawarar “ziri daya da hanya daya” da gina tashar cinikayya maras shinge ta Hainan。
A jawabin da ya gabatar, albarkacin bude wannan dandali na bana, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya ce a shirye kasar Sin take ta yi aiki da dukkan bangarori masu muradin gina shawarar “ziri daya da hanya daya” a matsayin wata muhimmiyar hanyar kawar da talauci da samun bunkasuwa.
Shugaban na Sin ya ba da shawarar sanya daidaito, da martaba juna da aminci tsakanin sassan kasashen duniya gaban komai, yayin raya alakar su.
Ya ce kasarsa, ba za ta taba neman yin babakere, ko fadadawa, ko yin tasiri na danniya ba, duk kuwa da irin karfi da ci gaban da za ta iya samu. Kaza lika Sin ba za ta shiga duk wata takara ta makamai ba. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)