logo

HAUSA

Aikin yiwa Sinawa dake Benin alluran rigakafin cutar COVID-19 zai sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu wajen yaki da cutar

2021-04-19 14:40:25 CRI

Aikin yiwa Sinawa dake Benin alluran rigakafin cutar COVID-19 zai sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu wajen yaki da cutar_fororder_0419-01

A halin yanzu, Sin tana kokarin samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 ga kasashe fiye da 10 da suke bukata ba tare da biyan kudi ba, kana ta fitar da alluran ga kasashen da suke son saye. Kasar Benin dake yammacin Afirka, tana daga daga cikin kasashe masu son sayen alluran rigakafin cutar na Sin. A ranar 21 ga watan Maris, alluran rigakafin cutar da Sin ta samar wa Benin ba tare da biyan kudi ba, da kuma alluran da Benin ta kara saye daga kasar Sin, sun isa filin jiragen sama na Cotonou dake kasar ta Benin. A kwanakin baya, an fara gudanar da aikin yiwa Sinawa dake kasar Benin alluran rigakafin cutar COVID-19, matakin da ya samu yabo, da maraba daga Sinawa dake kasar.

Jakadan Sin dake kasar Benin Peng Jingtao ya bayyana wa wakilin kafar CMG cewa, alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar, sun isa kasar a kan lokaci, kuma aikin yiwa Sinawa dake kasar Benin alluran, zai sa kaimi ga raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu wajen yaki da cutar.

A ranar 21 ga watan Maris, jakadan Sin dake kasar Benin Peng Jingtao, da ministan harkokin waje da hadin gwiwa na kasar Benin Agbenonci sun daddale takardar mika alluran rigakafin cutar COVID-19 na Sin ga kasar Benin, kana shi da ministan kiwon lafiya na kasar Benin, sun isa filin jiragen sama don maraba da zuwan alluran. Alluran sun jawo hankalin bangarori daban daban na kasar Benin sosai, har ma kafofin watsa labaru na kasar sun yi shiri kai tsaye game da isar alluran. Jakada Peng ya bayyana cewa,

“Bangarori daban daban na kasar Benin, sun yi farin ciki da zuwan alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar, inda minista Agbenonci ya jaddada hakan, yayin gudanar da bikin karbar alluran. A gun bikin, a madadin shugaban kasar da gwamnatin kasar da jama’arta, ya yi godiya ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, da gwamnatin kasar Sin, da kuma jama’arta. Ya ce samar da alluran da Sin ta yi ga kasar Benin, ya shaida zumunta dake tsakaninsu, da kuma hadin gwiwa mai zurfi a fannoni daban daban.”

Jakada Peng ya bayyana cewa, lokacin isar alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta samar, lokaci ne da za a gudanar da zaben shugaban kasar Benin. A wannan lokaci, ministan harkokin wajen kasar Benin ya gudanar da bikin musamman na karbar alluran, wanda hakan ya shaida cewa, Benin ta dora muhimmanci sosai ga alluran rigakafin cutar na kasar Sin. Ya ce,

“Abokaina da dama na kasar Benin, sun gaya mini ta hanyoyi daban daban cewa, suna son karbar alluran rigakafin cutar da Sin ta samar, suna begen alluran sosai. Ya zuwa yanzu, kasar Benin ta karbi alluran rigakafin cutar COVID-19 daga kasar Sin ne kadai. Alluran da Sin ta samar sun zo Benin a daidai.”

Tun daga ranar 6 zuwa 7 ga wannan wata, an kaddamar da aikin yiwa Sinawa dake Benin alluran rigakafin cutar COVID-19, inda Sinawan dake kasar suka karbar allura ta farko da aka yi musu, a wuraren da ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Benin ta bada iznin yin aikin. Jakada Peng ya yi bayani da cewa, gwamnatin kasar Beinin ta nuna goyon baya, da samar da gudummawar gudanar da aikin.

Game da hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 a tsakanin Sin da Benin kuwa, jakada Peng ya ambato wani labari dake cewa, wani ma’aikaci da ya yi ritaya daga kamfanin hadin gwiwar Sin da Benin, ya bada kudi da yawansu ya kai kudin shigarsa na wata daya, da ya samu a yayin yake aiki a kamfanin, don nuna goyon baya ga yaki da cutar COVID-19 a kasar Sin, a yayin tinkarar cutar da take yaduwa mai tsanani a kasar Sin, kana ya yi bayanin wani labari dake cewa, daliban kasar Benin dake karatu a kasar Sin, sun shiga aikin sa kai a kasar Sin, da kuma shiga aikin yaki da cutar COVID-19, bayan da suka dawo kasar Benin. A ganin jakada Peng, aikin yiwa Sinawa dake kasar Benin alluran rigakafin cutar COVID-19, zai sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu, wajen yaki da cutar zuwa wani sabon matsayi. Ya ce,

“Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Benin, wajen yaki da cutar COVID-19, ya shaida dangantakar sada zumunta da hadin gwiwa mai kyau a tsakaninsu. Bayan cutar ta barke, hadin gwiwarsu wajen yaki da cutar ya zama abun misali, kuma hadin gwiwarsu a fannin bayar da alluran rigakafin cutar, zai sa kaimi ga raya hadin gwiwarsu wajen yaki da ita, har zuwa wani sabon matsayi. An gudanar da aikin yiwa Sinawa dake kasar Benin alluran, wanda hakan ya shaida cewa, aka cimma nasarar yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a wannan fanni.

Hakan, na kuma kara bayyana dalilin da ya sa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, ke samun goyon baya daga jama’a, kana bangarorin biyu ke nuna kyakkyawar makoma ta hadin gwiwarsu.” (Zainab)