logo

HAUSA

Don me kasashen duniya suka kara maida hankali kan dandalin tattaunawa na kasashen Asiya a Bo’ao?

2021-04-19 20:53:35 CRI

Don me kasashen duniya suka kara maida hankali kan dandalin tattaunawa na kasashen Asiya a Bo’ao?_fororder_1

Bo’ao, wani karamin gari ne dake kudancin kasar Sin, wanda ya yi suna saboda shirya taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa a fannin tattalin arziki da ya taka rawa sosai a nahiyar Asiya. An fara taron bana ne tun daga jiya Lahadi, wanda ya samu halartar baki sama da 2600 daga kasashe da yankuna fiye da 60.

Shin me ya sa kasashen duniya suka kara maida hankali kan wannan dandalin tattaunawar?

Na farko, suna so su samu karfin gwiwa. A halin yanzu, tattalin arzikin kasashen Asiya da dama yana farfadowa, sakamakon matakan da suka dauka wajen dakile yaduwar cutar COVID-19 da raya tattalin arziki. Jiya, a yayin taron dandalin tattaunawar, an fitar da wani muhimmin rahoto mai taken “makomar tattalin arzikin Asiya gami da kokarin dunkule shi waje daya”, inda aka yi hasashen cewa, a bana tattalin arzikin Asiya zai habaka, har saurin karuwarsa zai zarce kaso 6.5 bisa dari.

Don me kasashen duniya suka kara maida hankali kan dandalin tattaunawa na kasashen Asiya a Bo’ao?_fororder_2

Har wa yau, kasashen duniya suna kokarin neman samun damar yin hadin-gwiwa. Asiya, daya ne daga cikin yankunan dake da makoma mai haske wajen samun ci gaba, kana ta fara zama mai yin kirkire-kirkiren fasahohi a tsarin tattalin arzikin duniya, da samun kasuwa da masu sayayya da yawa.

Daga shekaru 20 da suka gabata har zuwa yanzu, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen daga matsayin nahiyar Asiya a harkokin tattalin arzikin duniya. Wato saurin karuwar tattalin arzikin Sin ya taimaka sosai ga samun ci gaban Asiya, har ta zama “jigon farfado da tattalin arzikin Asiya” bayan cutar COVID-19.

A yayin taron dandalin tattaunawar da aka yi shekaru ukun da suka wuce, kasar Sin ta sanar da matakan fadada bude kofarta ga kasashen waje, da samar da kyakkyawar makoma ga nahiyar Asiya da ma duniya baki daya. Sai dai a halin yanzu, kasashen duniya suna son yin amfani da wannan dama, domin more sabbin dabaru da damammaki da kasar Sin ke samarwar nahiyar Asiya da ma duniya baki daya.(Murtala Zhang)