logo

HAUSA

‘Yan sandan Najeriya 144 sun isa kasar Somalia domin tallafawa aikin inganta tsaro

2021-04-19 13:23:58 CRI

‘Yan sandan Najeriya 144 sun isa kasar Somalia, inda za su fara aikin tallafawa wanzar da tsaro a kasar, karkashin tawagar AMISOM ta kungiyar tarayyar Afirka AU.

Da yake karin haske game da ayyukan da za su gudanar, babban jami’in tsare tsare na tawagar AMISOM a kasar Daniel Ali Gwambal, ya ce daga cikin jimillar ‘yan sandan, 30 za su yi aiki na tsawon shekara guda karkashin tawagar AMISOM, inda za a tura su yankunan Beletweyne dake jihar HirShabelle, yayin da sauran kuma za su yi aiki a sassan birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

Gwambal ya kara da cewa, sauran ‘yan sandan za su yi ayyukan tsaro da ba da kariya ga manyan jami’ai, da ba da horo, da tallafawa ‘yan sandan kasar wajen wanzar da zaman lafiya, za kuma su rika shiga ayyukan sintiri tare da takwarorin su na Somalia, domin ba da kariya ga muhimman cibiyoyin gwamnati, da muhimman wuraren taruwar jama’a.

Tawagar ta AU na fatan zuwan wannan rukuni na ‘yan sandan Najeriya kasar Somalia, zai bunkasa ayyukan kiyaye doka da oda, duba da cewa, za su yi aiki kafada da kafada da ‘yan sandan kasar, wajen tabbatar da an inganta tsaro a ‘yantattun yankunan kasar. (Saminu)